Tawagar FG sun isa Borno a kan kisan manoma 43 da Boko Haram tayi

Tawagar FG sun isa Borno a kan kisan manoma 43 da Boko Haram tayi

- Shugaban kasa Buhari ya aika wata tawaga zuwa Borno a kan kisan gillar da aka yi wa wasu manoma a jihar ta arewa

- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ne ya jagoranci tawagar wacce ta hada da kakakin Shugaban kasar, Garba Shehu da wasu ministoci

- Mayakan sun halaka akalla manoma 43 a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba

Wata tawaga ta gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, sun isa garin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Tawagar sun kai ziyarar jaje da ta’aziyya ne a kan kisan kiyashin da mayakan Boko Haram suka yi wa manoma 43 a yankin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere ta jihar.

An tattaro cewa manyan jami’an gwamnatun sun isa garin Maiduguri a ranar yau Litinin, 30 ga watan Nuwamba.

Tawagar FG sun isa Borno a kan kisan manoma 43 da Boko Haram tayi
Tawagar FG sun isa Borno a kan kisan manoma 43 da Boko Haram tayi Hoto: Ahmad Ibrahim Lawan
Asali: Facebook

Labarin ziyarar nasu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin labaran Shugaban majalisar dattawan, Ola Awoniyi ya saki a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalilin da yasa mayakan Boko Haram suka kashe mutum 110 a Zabarmari

A cewar sanarwar, mambobin tawagar sun hada da Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da ministan birnin tarayya, Mohammed Bello, da ministan sadarwa, Ali Pantami.

Sauran mambobin sun hada da mai ba kasa shawara a kan tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno (mai ritaya), karamin ministan noma, Mustapha Baba Shehuri da kakakin Shugaban kasa, Mallam Garba Shehu.

Legit.ng ta tattaro cewa tawagar sun samu tarba a filin jirgin sama daga mataimakin gwamnan jihar Borno, Usman Umar Gadafu.

Tawagar sun ziyarci Borno a madadin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin tarayya domin yin ta’aziyya ga iyalan mamatan, gwamnati da kuma mutanen Borno kan mummunan al’amarin.

KU KARANTA KUMA: Mun sanar da sojoji zuwan harin amma babu abunda aka yi, Al’umman Zabarmari

A gefe guda, Kungiyar gwamnonin Najeriya ta kwatanta kisan monoma 43 na kauyen Zabarmari a matsayin zalunci.

Sun fadi hakan ne ta bakin shugabansu, inda suka ce harin ya nuna gazawar tsaron kasar gaba daya.

Gwamna Fayemi ya ce wajibi ne su tattauna a kan yadda za su bullo wa lamarin a taron da za su yi na gaba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel