Kisan Zabarmari: Gwamnoni 36 sun kushe lamarin, sun bayyana matakin dauka

Kisan Zabarmari: Gwamnoni 36 sun kushe lamarin, sun bayyana matakin dauka

- Kungiyar gwamnonin Najeriya ta kwatanta kisan monoma 43 na kauyen Zabarmari a matsayin zalunci

- Sun fadi hakan ne ta bakin shugabansu, inda suka ce harin ya nuna gazawar tsaron kasar gaba daya

- Gwamna Fayemi ya ce wajibi ne su tattauna a kan yadda za su bullo wa lamarin a taron da za su yi na gaba

Duk gwamnonin jihohi 36 da ke karkashin NGF sun bayyana takaicinsu a kan kisan manoma 43 da aka yi a jihar Borno ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.

A wata takarda da suka saki a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba, wacce shugaban kungiyar, Gwamna Kayode John Fayemi na jihar Ekiti ya fitar, ya ce kisan zaluncin da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka yi, yana nuna zalunci da munin hali irin nasu.

Fayemi ya ce kisan zaluncin yana nuna tsananin gazawar tsaro a Najeriya, domin hakan yana nuna kasawar jami'an tsaro wurin kulawa da rayukan jama'a.

KU KARANTA: Tashan wutan lantarki ta kasa ta lalace, sunayen jihohin da rashin wuta zai shafa

Kisan Zabarmari: Gwamnoni 36 sun kushe lamarin, sun bayyana matakin dauka
Kisan Zabarmari: Gwamnoni 36 sun kushe lamarin, sun bayyana matakin dauka. Hoto daga @Kfayemi
Asali: Twitter

Ya kamata a ce an kara mikewa tsaye don kawo karshen wannan zaluncin. Tsohon CSO tun na mulkin janar Sani Abacha ya bayyana wasu miyagun kudurin wasu shugabannin Najeriya da suke tallafawa wurin baiwa 'yan ta'adda damar kai hari.

KU KARANTA: Sojin sama sun ragargaza mayakan ISWAP a Borno, sun watsa maboyarsu

A wani labari na daban, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar , ya bayyana alhininsa a kan kisan manoman shinkafa a karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, kuma ya yi kira ga jami'an tsaro da su yi gaggawar gyara tsarin harkar tsaro a kasar nan.

Atiku ya yi wannan kiran ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, jaridar The Punch ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: