Mun sanar da sojoji zuwan harin amma babu abunda aka yi, Al’umman Zabarmari

Mun sanar da sojoji zuwan harin amma babu abunda aka yi, Al’umman Zabarmari

- Wani mazaunin Zabarmari ya magantu game da lamarin da ke kewaye da harin da Boko Haram suka kai kauyen

- Abubakar Salihu ya ce rundunar soji za a daurawa laifi kan al’amarin da ya afku

- Sabon harin da mayakan suka kaddamar dai ya cika ne da manoman shinkafa

Mazauna garin Zabarmari sun sanar da sojoji game da harin da aka kai masu amma babu abunda aka yi, kamar yadda suka bayyana a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani mazaunin kauyen da ya tsira, wanda ya bayyana sunansa a matsayin Abubakar Salihu, ya bayyana cewa sun hango hatsarin bayan sun kama wani dan Boko Haram sannan suka mika shi ga jami’an tsaro.

“Mun sanar da sojoji cewa mambobinmu sun gano yan Boko Haram da yawa amma babu abunda aka yi game da hakan.

Mun sanar da sojoji zuwan harin amma babu abunda aka yi, Al’umman Zabarmari
Mun sanar da sojoji zuwan harin amma babu abunda aka yi, Al’umman Zabarmari Hoto: @GovBorno
Source: Twitter

“Ranar bakin ciki ne garemu a Zabarmari; da an dakile harin amma sojoi suka ki daukar mataki kan bayanan da muka basu,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Ku tashi tsaye ku kare kanku daga yan ta’adda, kungiyar CNG ga yan arewa

Wani manomin shinkafa, Mohammed Alhaji, ya ce mutanen da aka kashe sun dukufa wajen girbe shinkafa lokacin da mayakan suka far masu sannan suka tattara su.

“Da gangan ne don tabbatar da ganin cewa bamu girbe albarkatun gonanmu ba. Muna bukatar gwamnatin tarayya ta taimake mu sannan ta kare mana rayukanmu,” in ji shi.

Legi.ng ta tattaro cewa harin ya wakana ne a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba, yayinda mayakan Boko Haram suka zagaye manoma a gonakinsu sannan suka yi masu yankan rago.

Gaba daya gawawwakin da aka samu a wuri guda bayan harin ya kasance 43. Gawawwakin da aka samo a wasu wuraren ya daga yawan mutanen da suka mutu zuwa 110.

Daily Trust ta tattaro cewa kimanin makonni biyu da suka gabata, rundunar soji da yan sa kai sun kama wasu mayakan Boko Haram a kusa da garuruwan da abun ya shafa.

A gefe guda, tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke ya yi zargin cewa mafi akasarin makaman yan ta’addan Boko Haram ana samun su ne daga jami’an tsaro.

PM News ta ruwaito cewa da yake magana a tashar Channels TV, Duke ya yi kira ga gwamnatin tarayya a kan ta binciki rundunar tsaro sannan ta fitar da bara gurbi.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel