Jam’iyyar APC ta kafa kwamiti da zai hukunta Hilliard Eta a Kuros Ribas

Jam’iyyar APC ta kafa kwamiti da zai hukunta Hilliard Eta a Kuros Ribas

- Hilliard Eta ya kai karar Jam’iyyar APC kotu a kan tsige Adams Oshiomhole

- Eta ya na kalubalantar matakin da aka dauka na yin waje da majalisar NWC

- Jam’iyyar APC ta ce za ta binciki zargin da ake yi wa Hilliard Eta na yin laifi

Jam’iyyar APC ta reshen jihar Kuros-Riba ta yanke hukuncin cewa za ta kafa wani kwamiti da zai binciki Hilliard Eta, sannan ya ladabatar da shi.

Ana zargin Mista Hilliard Eta, tsohon shugaban jam’iyyar APC na yankin Kudu maso kudu, da laifin yi wa jam’iyya makarkashiya da zagon-kasa.

Hilliard Eta ya shigar da kara a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2020, ta hannun lauyansa, Onyechi Ikpeazu SAN, ya na kalulabalantar tsige su da aka yi.

KU KARANTA: Buhari ya sa a ruguza NWC, an nada sababbin shugabanni a APC

Eta ya fada wa kotu cewa bai amince da sauke su da aka yi daga kan mukamansu ba. Eta yana cikin ‘yan majalisar NWC ta Adams Oshiomhole.

Lauyan da ya tsaya wa Hilliard Eta, ya roki Alkalin babban kotun tarayya a Abuja da ya kai wa karar, a hana shugabannin rikon kwarya rike jam’iyya.

A dalilin haka jam’iyyar APC a jihar da Hilliard Eta ya fito, ya fitar da jawabi ta bakin shugabanta, Mathew T. Mbu da Ministan wuta, Prince Jedy Agba.

Mai girma karamin Ministan harkar wuta na kasa, Jedy Agba ya na cikin jagororin APC a jihar.

KU KARANTA: Buhari: Abin da ya sa aka yi waje da Oshomhole a APC

Jam’iyyar APC ta kafa kwamiti da zai hukunta Hilliard Eta a Kuros Ribas
Jam’iyyar APC ta na taron NEC Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

Sanata Mathew T. Mbu, mai rike da jam’iyyar APC a jihar Kuros Riba, ya bayyana cewa Eta bai bi hanyar da ta dace wajen shawo kan rigimar gida ba.

A kan kin bin abin da dokar APC ta tanada da kuma yi wa jam’iyya zagon-kasa ne za a kafa kwamiti da zai binciki Eta, ya kuma zartar da hukunci.

Tun a baya kun ji cewa wasu cikin ‘yan majalisar NWC ta jam’iyyar APC da aka ruguza a wajen wani taron NEC, su na duba yiwuwar kai jam'iyya kotu.

Wadannan fusatattun 'ya 'yan jam'iyya sun yi ta tuntubar Lauyoyi da masu ruwa da tsaki domin yanke shawara game da matakin da za su dauka a APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel