Buhari ya ce a rusa Majalisar NWC a taron NEC, an nada gwamnan Yobe shugaban rikon kwarya

Buhari ya ce a rusa Majalisar NWC a taron NEC, an nada gwamnan Yobe shugaban rikon kwarya

Yanzu nan mu ke samun labari cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a sallami daukacin Majalisar NWC.

Jam'iyyar APC ta yanke wannan hukunci ne a wurin taron Majalisar NEC da ake yi yanzu haka a babban birnin tarayya.

NEC wanda ita majalisar koli a jam’iyyar ta yi na’am da shawarar da shugaban kasa ya bada, ta ruguza majalisar NWC.

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa ya bayyana wannan mataki da jam’iyyar APC ta dauka a shafinsa na Twitter dazu.

Kamar yadda hadimin shugaban kasar ya nuna, daukacin majalisar NEC ta yi na’am da wannan mataki da aka zartar.

Bayan an ruguza majalisar NWC mai alhakin gudanar da harkokin jam’iyya, an nada wani kwamitin rikon kwarya.

KU KARANTA: Gwamnonin APC su na goyon bayan taron NEC

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni shi ne shugaban kwamitin rikon kwarya wanda zai rike jam’iyyar na ‘dan lokaci.

Bisa dukkan alamu, Alhaji Mai Mala Buni zai gudanar da zaben sababbin shugabannin jam’iyya watau NWC nan gaba.

Mala Buni shi ne tsohon sakataren jam’iyya na kasa, kuma tun daga lokacin da ya bar ofis, ake samun rigingimu a APC.

Da wannan mataki da aka dauka, babu wanda zai rike APC tsakanin Adams Oshiomhole, Victor Giadom da Abiola Ajimobi.

Hakan na nufin ‘ya ‘yan APC za su sake sabon shiri domin a shirya babban zaben shugabannin na kasa nan da wani lokaci.

Wadanda su ka halarci taron sun hada shugabn kasa da mataimakinsa, Ahmad Lawan, da Femi Gbajabiamila da gwamnonin 15.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng