Abubuwa da su ka sa Buhari ya kwarewa NWC baya wajen dinke barakar APC

Abubuwa da su ka sa Buhari ya kwarewa NWC baya wajen dinke barakar APC

Jaridar Vanguard ta ce dalilan da su ka jawo shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rinjayar da matakin sauke shugabannin jam’iyyar APC na kasa ya bayyana mata a daren Juma’a.

Rahotanni sun bayyana cewa NEC ta ruguza majalisar NWC ta shugabannin jam’iyyar APC ne domin gujewa barkewar mummunan rikicin da ke daf da cin APC mai mulki.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rigimar da ta kunno wuta a cikin gidan APC da rikicin da zai cinye jam’iyyar, don haka majalisar NEC ta dauki matakin da ya zama dole.

A taron gaggawan da NEC ta shirya a ranar Alhamis, an sauke daukacin shugabannin APC na kasa, aka nada kwamitin rikon kwarya wanda zai gudanar da sabon zaben shugabanni.

Majiyar ta ce shugaban kasar ya bada shawara a sauke shugabannin APC da ke karkashin jagorancin Adams Oshiomhole ne saboda irin rikon da su ke yi wa jam’iyyar.

“Ana zargin Adams Oshiomhole ya maida jam’iyyar kamar ta gidansa, inda ya ke yin abin da ya ke so tare da wani daga cikin wadanda aka kafa jam’iyyar da su.” Inji majiyar.

KU KARANTA: APC: Yadda ta kaya da Giadom a wajen taron NEC

Abubuwa da su ka sa Buhari ya kwarewa NWC baya wajen dinke barakar APC
Adams Oshiomhole
Asali: Depositphotos

“Mutane 17 daga cikin ‘yan majalisar NWC su na tare da Adams Oshiomhole da wannan jigo.” Rahotanni sun ce wadanda su ke tare da Victor Giadom a NWC ba su wuce mutane biyu ba.

Ya ce: “Ana ta sabawa dokokin jam’iyya, Oshiomhole shi kadai ya na daukar matakai da-dama da ya kamata ace NEC ta sa hannu.” Ana zargin NWC da aka rusa ta na da goyon bayan Bola Tinubu.

Wannan ‘dan jam’iyyar ya fadawa jaridar cewa: “Abubuwa ba za su tafi a haka ba. Dole shugaban kasa (Muhammadu Buhari) ya ceci jam’iyyar."

A taron da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa, an nada Mai Mala Buni a matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya wanda zai rike jam’iyyar na lokaci kadan.

A wajen wannan zama da aka yi, an kuma nada Sanata John Akpanudoedehe ya zama Sakataren kwamitin. Tuni ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya kaddamar da kwamitin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel