Mu Jonathan ke yi wa aiki, APC ta zolayi PDP

Mu Jonathan ke yi wa aiki, APC ta zolayi PDP

- Jam'iyyar APC ta yi ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na yi mata aiki

- Mataimakin sakataren watsa labarai na APC, Yekini Nabena ne ya yi wannan furucin yayin hira da aka yi da shi a wani shirin talabijin

- Ya bada misali da tafiye-tafiyen da Goodluck Jonathan ke yi kasashen Afirka madadin gwamnatin Buhari

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a Najeriya, a ranar Juma'a 27 ga watan Nuwamba ta cacaki jam'iyyar PDP kan gazawarta a matsayin jam'iyyar hamayya.

APCn ta kuma yi ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yana yi wa jam'iyyar ta gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari aiki domin shi dattijo ne mai 'son cigaban kasa'.

Mataimakin sakataren watsa labarai na kasa na jam'iyyar APC, Yekini Nabena ne ya ambata hakan a ranar Juma'a yayin hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today da gidan talabijin na Channels, The Punch ta ruwaito.

Mu Jonathan ke yi wa aiki, APC ta zolayi PDP
Mu Jonathan ke yi wa aiki, APC ta zolayi PDP. Hoto: @Buharisallau1
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama

A baya bayan nan, wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun ziyarci tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a gidansa da ke Abuja a ranar Juma'a da ta gabata.

Wannan ziyarar da jiga-jigan na APC suka kai wa tsohon shugaban kasar wadda ya yi takarar shugabancin kasa karkashin PDP a 2011 da 2015 ya janyo maganganu game da zaben 2023.

Jonathan ya sha kaye hannun Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 inda ya amsa shan kayensa ya mika mulki ga Buhari.

Jam'iyyar na PDP ta ce ziyarar da jiga-jigan APC suka kai wa tsohon shugaban kasar a ranar da ya cika shekaru 63 a duniya ya nuna 'sun matsu'.

DUBA WANNAN: Kotu ta yanke wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa hukuncin shekaru 3 a gidan maza

Amma a martanin da ya yi ranar Juma'a, Nabena ya ce, "Ba matsuwa muka yi ba. Goodluck Jonathan ya dade yana yi wa wannan gwamnatin aiki, ya yi ta tafiye-tafiye zuwa kasashen Afirka. Idan shi ba mutum mai son cigaba bane, da bai dinga yi wa wannan gwamnatin aiki ba."

A wani labarin daban, kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEFG, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata a bangaren gine-ginen tituna a yankin ta.

Kungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel