FG bata yi mana adalci, in ji gwamnonin Arewa maso gabas
- Gwamnonin jihohin Arewa ta Gabas sunyi korafi game da rashin adalcin da suke ce gwamnatin tarayya na musa a bangaren aikin titi
- Gwamnonin karkashin kungiyarsu, NEFG, sunyi zargin cewa an yi watsi da ayyukan tituna a yankin a wasu wuraren kuma aikin na tafiyar hawainiya
- Don haka, NEFG, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta duba batun, ta bada umurnin cigaba da ayyukan tituna da aka bayar a yankin nan take
Kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEFG, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata a bangaren gine-ginen tituna a yankin ta kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Kungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.
DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama ɗan aikin gida da ya kashe maigidansa a Nasarawa (Hotuna)
Kazalika, kungiyar ta nuna rashin dadinta kan 'tafiyar hawainiya ko rashin samun cigaba' kan yadda ake gudanar da kwangilolin ayyukan titi da aka bayar a yankunan.
"Kungiyar ta lura cewa ma'aikatan ayyuka da gidaje ta gwamnatin tarayya bata yi wa yankunanta adalci a bangaren gine ginen tituna.
KU KARANTA: Kotu ta yanke wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa hukuncin shekaru 3 a gidan maza
"Har wa yau, kungiyar bata jin dadin jan-kafa ko rashin cigaban ayyukan tituna da aka bada a yankunan ta kuma ta yi kira da cewa a cigaba da ayyukan nan take tare da yin bita kan sauran ayyukan tituna da aka bada a yankin," a cewar sakon bayan taron.
A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng