Kotu ta yanke wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa hukuncin shekaru 3 a gidan maza

Kotu ta yanke wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa hukuncin shekaru 3 a gidan maza

- Kotu a kasar Uganda ta yanke wa tsohon dan takarar shugaban kasa hukuncin shekaru uku a gidan maza

- Kotun ta yanke wa Ivan Samuel Ssebadduka hukuncin ne saboda kalaman batanci da ya yi amfani da su kan alkalan

- Alkalin Alkalai na kasar Owinyi-Dollo ya ce ya zama dole duk wanda zai soki alkalai ya yi hakan bisa gaskiya da adalci

Kotun koli na kasar Uganda ta daure tsohon dan takarar shugaban kasa saboda amfani da kalaman cin mutunci a kansu ciki har da kiransu 'sakarkarun da basu iya aiki ba'.

An yanke wa Ivan Samuel Ssebadduka hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekaru uku saboda raina kotu a cewar rahotannin da kafafen watsa labarai na kasar.

An yanke wa tsohon dan takarar shugaban kasa hukuncin shekaru 3 a gidan maza
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Ivan Samuel Ssebadduka. Hoto daga @TheNationNews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yan bindiga sun afka wasu kauyukan uku a Zamfara, sun kashe uku, mazauna gari sun tsere

Mista Ssebadduka tun a watan Satumba ya shigar da kara a kotun kolin inda ya ke neman a soke tanadin da doka tayi na cewa dukkan masu neman takarar shugaban kasa sai sun samu sa hannu daga wani adadin mutane kafin su tsaya takarar.

Ya kuma bukaci kotun ta dage dokokin kariya da ma'aikatar lafiya na kasar ta saka wa 'yan takara masu yajin neman zabe don takaita yaduwar annobar korona.

Ya yi amfani da kalamai na cin mutunci a lokacin da ya ke kare korafin da ya shigarwa kotu a gaban alkalan.

DUBA WANNAN: Zaben 2023: Jigo a Arewa dan APC ya bukaci a baiwa dan kudu takara

An ruwaito cewa Alkalin Alkalai, Alfonse Owinyi-Dollo na kasar yana cewa, idan za soki alkalai ya kamata ayi hakan bisa gaskiya da adalci kuma kada hakan ya zama damar taka hakokin wasu.

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel