Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama

Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama

- Sojojin Najeriya sunyi nasarar kashe wasu hatsabiban 'yan bindiga 3 da ke adabar mutanen Abaji a jihar Benue

- Sojojin sun kai farmaki mabuyar 'yan bindigan ne bayan samun sahihan bayannan sirri inda suka musu dirar mikiya tare da cin galaba kansu

- Har wa yau, sojojin sunyi nasarar damke wasu mutum biyu da ake zargin su ke ruruta wutar rikicin makiyaya da manoma a Atiyagiso

Dakarun sojojin Najeriya na musamman na Operation Whirl Stroke na cigaba da samun nasarori a yunkurinsu na kawar da ayyukan bata gari a yankin Arewa ta tsakiya.

A jiya Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2020, bayan samun sahihan bayannan sirri, dakarun sun kai farmaki mabuyar wasu 'yan bindiga da suka dade suna adabar al'ummar Abaji da ke karamar hukumar Katsina Ala ta Jihar Benue.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama
Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama. Hoto: @DefenceInfoNG
Source: Twitter

Sojojin sunyi arangama da 'yan bindigan a kusa da kauyen Asogo nan take suka fara musayar wuta daga baya 'yan bindigan suka tsere cikin daji.

DUBA WANNAN: Kotu ta yanke wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa hukuncin shekaru 3 a gidan maza

Dakarun sojojin sun ci galaba a kan 'yan bindigan inda suka kashe guda uku sannan suka kwato bindigu kirar pistol guda 3 da harsashi na musamman guda 11.

Kakakin hedkwatan tsaro Manjo Janar John Enenhe ne ya bayyana hakan cikin wani sanarwa da ya fitar ta shafin Twitter na hedkwatar tsaro a ranar 27 ga watan Nuwamba

Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama
Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama. Hoto: @DefenceInfoNG
Source: Twitter

Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama
Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama. Hoto: @DefenceInfoNG
Source: Twitter

Har wa yau, a ranar 26 ga watan Nuwamba, sojojin sector 3 sun kai sumame gidajen wasu mutane da ake zargi da hannu a rikicin makiyaya da manoma a garin Atiyagiso a karamar hukumar Doma na Jihar Nasarawa.

KU KARANTA: Yan bindiga sun afka wasu kauyukan uku a Zamfara, sun kashe uku, mazauna gari sun tsere

Yayin sumamen sun kama mutum biyu da ake zargi, Abdulkareem da Mohammed Sani wadda suka amsa cewa suna da hannu cikin rikicin sannan suka mika su ga 'yan sanda.

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel