2023: Ku kunyata ni ta hanyar mikawa kudu maso gabas tikitin shugaban kasa, Umahi ga PDP
- Gwamna Umahi ya sake aika wani muhimmin sako zuwa ga tsohuwar jam’iyyarsa, PDP, gabannin 2023
- Gwamnan na jihar Ebonyi ya ce yana zuba ido don ganin jam’iyyar adawar ta kunyata shi ta hanyar mika tikitinta na shugaban kasa a 2023 ga yankin kudu maso gabas
- Gwamnan ya kuma bukaci jam’iyyar da ta janye daga kai masa hari
Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya ce yana jira don ganin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bashi kunya ta hanyar mika tikitinta na shugaban kasa a 2023 zuwa yankin kudu maso gabas.
Jaridar Sun ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da Sanata Orji Uzor Kalu, tsohon gwamnan Abia, ya shirya masa wani taron cin abincin dare a Abuja a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba.
Ku tuna cewa Umahi ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, inda ya bayyana rashin adalci da PDP ke yi wa kudu maso gabas a matsayin dalili.
KU KARANTA KUMA: Dattijo ya roƙi kotu ta ƙwato masa N50,000 daga iyayen budurwar da aka hana shi auren ta
Ya yarda cewa ya kamata PDP ta sakawa yankin kudu maso gabas kan biyayyar da take mata ta hanyar mika mata tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023.
Umahi ya kuma fada ma PDP cewa ta daina kai masa hari, cewa babu wani amfani kan hakan.
Gwamnan na jihar Ebonyi ya ce bai caccaki jam’iyyar mai adawa ba tunda ya koma APC illa kawai ya bayyana rashin adalcin da take yi wa yankin kudu maso gabas.
Sai dai, ya kara da cewa tsohuwar jam’iyyar nasa tana da hakkin yin fushi, inda yace ba zai hada kowani lamura da shugabannin adawa ba.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika a Abuja
A nashi jawabin, Sanata Kalu ya yi watsi da rahotannin kafofin watsa labarai na cewa wasu jiga-jigan APC basu ji dadin dawowar Gwamna Umahi jam’iyyar mai mulki ba, ya ce karya ne.
A gefe guda, darekta janar na PGF, Dr. Salihu Lukman, yace fom din takarar jam'iyyar APC zai fita don duk masu neman wata kujera su nema, jaridar The Punch ta wallafa hakan.
Ya ce siyasa ta kunshi gasa ne, gasar da ake yi a siyasar da, yanzu ba a yinta. Ya sanar da manema labarai hakan a Abuja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng