Yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika a Abuja

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika a Abuja

- Wasu da ake zaton yan bindiga ne sun yi awon gaba da wani limamin cocin Katolika a Abuja

- Rundunar yan sandan birnin tarayya ta tabbatar da lamarin wanda ya afku a ranar Lahadi

- Tuni dai jami'an tsaro suka bazama domin ceto shi tare da kama masu laifin

Wani rahoto da jaridar TheCable ta wallafa ya nuna cewa yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika a babbar birnin tarayya Abuja.

An tattaro cewa an sace limamin cocin ne a kewayen Yangoji, wani gari da ke kusa da yankin Kwali a babbar birnin tarayya, a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba.

Da take tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, rundunar yan sandan birnin tarayya ta bayyana cewa ta kaddamar da wani aiki domin ceto limamin cocin.

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika a Abuja
Yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika a Abuja Hoto: Getty Images
Asali: Twitter

Miriam Yusuf, mai magana da yawun rundunar, ta bukaci mazauna yankin birnin tarayya da su kwantar da hankalinsu sannan su kai rahoton duk wani yunkuri da basu gamsu da shi ba.

KU KARANTA KUMA: FG ta bayyana lokacin da Najeriya za ta fita daga karayar tattalin arziki

Yusuf ta bayyana cewa yan sanda a birnin tarayyar kasar sun jajirce domin kare rayuka da dukiyoyin mazauna yankin.

“Kwamishinan yan sanda na birnin tarayya, Bala Ciroma, ya kaddamar da wani farauta don ganowa tare da kama masu laifin,” in ji ta.

“Yayinda take bukatar mazauna yankin da su zamo masu lura da kai rahoton duk wani motsi da basu gamsu da shi ba a kan lokaci, rundunar na burin jaddada jajircewarta wajen kare rayuka da dukiyoyi a birnin tarayya.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsohuwar kwamishinar lafiya ta jihar Bauchi Zuwaira Hassan ta rasu a hatsarin mota

Lamarin rashin tsaro a kasar ya san gwamnati da al’umman kasar cikin damuwa.

A wani labari na daban, mun ji cewa an saki daliban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, jihar Kaduna su tara da aka yi garkuwa da su.

An yi garkuwa da su ne a wani hari da aka kai wa masu motoci a babbar hanyar Kaduna-Abuja.

Dickson Oko, daya daga cikin daliban wanda ya tsere amma ya samu rauni sakamakon harbin bindiga, ya ce dama masu garkuwan sun tuntubi iyalan daliban sannan suka bukaci naira miliyan 30 kafin a saki kowannensu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel