2023: DG na PGF a karkashin APC ya bayyana yankin da jam'iyyar za ta mika tikitin ta

2023: DG na PGF a karkashin APC ya bayyana yankin da jam'iyyar za ta mika tikitin ta

- A ranar Litinin, darekta janar na PGF, Dr Salihu Lukman, ya ce kwanan nan APC za ta fara sayar da fom din takara

- A cewarsa, ko shugaba Buhari bai da alhakin zabar dan takara, al'umma ne suke da wannan damar

- Ya ce, kowa zai iya siyan fom kuma ya fara kamfen don matsawar aka zabeshi, to shi za a tsayar

A ranar Litinin, darekta janar na PGF, Dr. Salihu Lukman, yace fom din takarar jam'iyyar APC zai fita don duk masu neman wata kujera su nema, jaridar The Punch ta wallafa hakan.

Ya ce siyasa ta kunshi gasa ne, gasar da ake yi a siyasar da, yanzu ba a yinta. Ya sanar da manema labarai hakan a Abuja.

Lukman ya kula da yadda kungiyar ta dage wurin bunkasa. Ga dukkan alamu, PGF za ta tsayar da 'yan takara nagari a matsayi daban-daban, a zaben 2023.

2023: DG na PGF a karkashin APC ya bayyana yankin da jam'iyyar za ta mika tikitin ta
2023: DG na PGF a karkashin APC ya bayyana yankin da jam'iyyar za ta mika tikitin ta. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Ya ce ba jam'iyyar APC ko Shugaba Buhari ne zai bayar da umarnin inda za a bai wa damar tikitin ba.

KU KARANTA: Batan dabon Maina: Kotu ta bukaci a adana mata Sanata Ndume a gidan maza

Lukman ya ce, "Yanayin yadda APC take taka babbar rawa ya sanya kullum take samun karbuwa ta ko ina.

"Misali, kalli yadda hankalin kowa ya karkata a kan jam'iyyar, don a ga yadda za ta kaya a 2023 ko kuma wani zabe da zai zo."

Yace idan a matsayinka na dan takara ba za ka iya dagewa wurin samun karbuwa a wurin mutane ba, to ya rage gareka.

"Abinda na ke so kowa ya sani shine, shugaba Buhari ba shi da alhakin zabar wani a jam'iyya, mutane ne keda wannan alhakin.

"Shiyasa mutane duk suna ta kiyasi, kowa da wanda yake zaton shi za a tsayar a zaben 2023, sai an tantance wanda zai tsaya takara a APC.

"Idan mutum dan siyasa ne, kawai ya fara kamfen, kowa zai iya samun nasara idan ya dage." yace.

KU KARANTA: Tsintar gawar shugaban APC: Buhari ya yi martani tare da aike wa jami'an tsaro sako

Yayi magana a kan komawar gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, jam'iyyar APC, wanda yace hakan babbar nasara ce, duk da suna cewa 'yan kudu maso gabas ba sa son jam'iyyar APC.

A wani labari na daban, hankula sun karkata a kan jam'iyyar APC ta jihar Legas a kan zaben 2023, da kuma hanyoyin dakatar da shugaban jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu.

Duk da dai har yanzu zaben 2023 yana da tazara, jam'iyyar APC ta jihar ta shiga tararrabi a kan yadda masu fadi a ji suka fara nuna kwadayin mulkin jihar Legas, karara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel