Ganau: Yadda shugaban APC na jihar Nasarawa ya yi ta ihun 'a taimaka min' kafin a kashe shi

Ganau: Yadda shugaban APC na jihar Nasarawa ya yi ta ihun 'a taimaka min' kafin a kashe shi

- A ranar Lahadi ne aka wayi gari da samun labarin yin garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Philiph Schekwo

- Jim kadan baya samun labarin sace shi, sai ga shi rahotanni sun sanar da cewa an tsinci gawarsa

- Wani shaidar gani da ido, da ya ikirarin cewa komai ya faru akan idonsa, ya yi karin bayani a kan mutuwar Schekwo

Sabbin batutuwa sun ɓullo kan yadda aka kashe, Philip Schekwo, shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa da ƴan bindiga suka sace shi, sannan suka kashe shi.

Majiyoyi sun bayyana cewa masheƙan sun zo gidan Schekwo da ke kan titin Kurikyo kusa da cocin Dunamis da ke Bukan Sidi a garin Lafia da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare 11pm inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Ƙarar bindigun su suka tashi Schekwo daga barci,nan ya gano akwai matsala,take ya fara kiran hukumomin tsaro amma basu ɗaga ba har aka ƙwamushe shi.

DUBA WANNAN: Atiku ya fadi daliin da yasa tattalin arzikin Nigeria ke karyewa a karkashin mulkin Buhari

Ganau: Yadda shugaban APC na jihar Nasarawa ya yi ta ihun 'a taimaka min' kafin a kashe shi
Ganau: Yadda shugaban APC na jihar Nasarawa ya yi ta ihun 'a taimaka min' kafin a kashe shi @Thecable
Asali: Twitter

Mr Joseph Gudu,maƙwabcin marigayin ne,yace akan idonsa komai ya faru domin kuwa yana hango komai ta tagar gidansa.

Ya bayyana yadda ƴan bindigar suka yi amfani da garma wajen karya ƙofar gidan da tagogin gidan.

DUBA WANNAN: 2023: Ba zamu taba lamunta a dauki Kirista daga arewa a matsayin dan takarar mataimaki ba; jigo a APC, Farfesa Mahuta

"Matar marigayin, ƴaƴansa da shi kanshi sun kira jami'an tsaro yafi a ƙirga, sai dai ba wanda ya amsa kiran nasu.

"Suna ta ihu da karajin taimako!, a taimaka!! Amma ba jami'in tsaron da ya zo ceto ko agaza musu. Ƴansanda ba su da niyyar ɗaga kiransu.

"Sun kwashe mintuna 49 kafin su sami damar shiga ɗakin kwanan marigayin bayan sun ci ƙarfin jami'an tsaron da ke bashi kariya, sannan suka ɗauke shi," a cewarsa.

A baya Legit.ng Hausa ta wallafa labarin yadda wasu 'yan bindiga suka kutsa kai cikin gidan dan majalisar wakilai, Abubakar Kusada, a jihar Katsina.

Bayan shigarsu gidan, 'yan bindigar sun nemi ina mahaifiyar dan majalisar ta ke, kasancewar ba ta gidan, 'yan bindigar sun yi awon gaba da 'yan uwan Honarabul Kusada guda biyu tare da raunata wani guda.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel