Katsina: 'Yan bindiga sun afka gidan dan majalisar wakilai, sun sace mutum biyu

Katsina: 'Yan bindiga sun afka gidan dan majalisar wakilai, sun sace mutum biyu

- Har yanzu 'yan bindiga na cigaba da kai hare-hare tare da kashe mutane ko yin garkuwa da su a sassan jihar Katsina

- A wannan karon, 'yan bindigar sun afka gidan Abubakar Kusada, mamba a majalisar wakilai daga jihar Katsina

- 'Yan bindigar sun yi awo gaba da biyu daga cikin 'yan uwan dan majalisar bayan basu samu mahaifiyarsa ba

A ranar Lahadi ne wasu 'yan bindiga a Katsina suka afka gidan Abubakar Kusada, mamba a majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kusada/Inagawa/Kankiya tare da yin awon gaba da mutane biyu daga gidan.

Jaridar Punch ta wallafa cewa an sace Sulaiman Musa da Talatu Musa tare da raunata Jamilu Musa bayan sun kutsa kai cikin gidan Honarabul Kusada.

Mazauna garin sun sanar da cewa 'yan bindigar sun fara tambayar ina mahaifiyar dan majalisar ta ke bayan sun shiga gidan.

DUBA WANNAN: An shiga har cikin Caji Ofis an harbe dan sanda a babban Ofishinsu da ke Ado

Daga baya 'yan bindigar sun yi awon gaba da 'yan uwan dan majalisar guda biyu bayan sun gaza samun mahaifiyarsa.

Katsina: 'Yan bindiga sun afka gidan dan majalisar wakilai, sun sace mutum biyu
Katsina: 'Yan bindiga sun afka gidan dan majalisar wakilai, sun sace mutum biyu Hoto: Hon. Abubakar Kusada
Asali: Facebook

Kazalika, 'yan bindigar sun raunata daya daga cikin 'yan uwan dan majalisar mai suna Jamilu yayin da ya yi yunkurin tserewa.

Majiya masu yawa, da ke da kusanci da dangin dan majalisar, sun ce Honarabul Kusada da mahaifiyarsa basa garin yayin da 'yan bindigar suka dira gidan.

DUBA WANNAN: 2023: Ba zamu taba lamunta a dauki Kirista daga arewa a matsayin da takarar mataimakin shugaban kasa ba; Fafesa Mahuta

Daya daga cikin majiyar ta bayyana cewa dan majalisar, wanda ke Katsina a lokacin da abin ya faru, ya koma Abuja bayan ya sanar da faruwar lamarin a babban Ofishin 'yan sanda da ke Kusada.

Ba'a samu jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, DSP Gambo Isa, ba a kan batun saboda ba'a same shi ba da aka kira lambar wayarsa ta hannu ba.

A baya Legit.ng Hausa ta rawaito cewa rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa an kubutar da manyan 'yan sanda tara, dukkansu ASP, da aka sace tun ranar takwas ga watan Nuwamba na wannan shekarar a jihar Katsina.

An sace manyan 'yan sandan ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, Maidugurin jihar Borno.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel