2023: Abinda arewa ta ke bukata bayan mulkin Buhari; jigo a APC, Farfesa Mahuta

2023: Abinda arewa ta ke bukata bayan mulkin Buhari; jigo a APC, Farfesa Mahuta

- Tuni an fara kulle-kulle da maganganu a kan gwamnati ta gaba da zata karbi mulki daga hannun Buhari

- Yanki arewacin Nigeria ba zai manta da kalubalen tsaro da ya tsinci kansa ba a mulkin Buhari

- Farfesa Mahuta ya ce jahiltar ilimin Boko da rashin aikin yi ga matasa sune makamashin matsalolin arewa

Farfesa Sahabi Ɗanladi Mahuta, jigo kuma uba a jam'iyyar APC, shararren malamin addinin Musulunci ne kuma Farfesa a fannin kimiyyar sinadaran halittu (Biochemistry) a jami'ar Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Haka kuma Farfesa Mahuta shine shugaban ƙungiyar cigaban jihar Kebbi (KDF), wata ƙungiya mai tsawatarwa da jawo hankalin shugabanni domin yin abin da ya dace daga ɓangarori da dama a cikin al-umma.

Jim kaɗan bayan kammala taron shugabannin Musulmi a birnin Abuja, Farfesa Mahuta ya yi tambihi da tsokaci kan batutuwan da aka tattauna a taron yayin wata hira da manema labarai.

KARANTA: Kotu ta janye belin Abdulrasheed Maina, ta bada umarnin a kama shi duk inda aka gan shi

An tambayi Farfesa Sahabi kamar haka; "daga cikin jigon abubuwan da suka assasa matsalar tsaro a arewa akwai tsarin Almajiri, wanda Almajirai da dama ke shiga ayyukan ta'addanci, Boko Haram, da ɓarayin mutane da shanu, me ka ke tunanin za'a yi domin a shawo kan matsalar?

2023: Abinda arewa ta ke bukata bayan mulkin Buhari; jigo a APC, Farfesa Mahuta
2023: Abinda arewa ta ke bukata bayan mulkin Buhari; jigo a APC, Farfesa Mahuta
Asali: UGC

Ya bada amsa kamar haka; "ya kamata gwamnati ta san da tsarin Almajiri a arewacin Najeriya a matsayin tsarin ilimantarwa ta hanyar tattara alƙaluman makarantun Almajirai a ƙasar nan.

"Waɗanda suke kai ƴaƴansu makarantun allo na Almajiranci suna ganin hakan a matsayin farilla wato wajibi don neman ilimi a addinance.

KARANTA: Karin albashin Malamai: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitin aiwatarwa

"Dukkanmu mun san tsarin Almajiranci yana tattare da naƙasu saboda karatun kawai suke ba tare da sanin ma'anar karatun ba.

"Domin sanin ma'anar dole sai mun dawo baya an gabatar da tsarin Yaren Ingilishi, ilmin Lissafi da ƙidaya da kuma sana'o'i wanda hakan zai sa su amfani al-umma baki ɗaya.

A matsayinka na sannanen malamin addinin musulunci,shin akwai wata gudunmawa da addini zai bayar wajen warware matsalar Almajiri a arewacin Najeriya?

"Eh, a maida tsarin cikin tsarin koyo ga Musulman arewa, a canja tsarin, ko mafi ƙaranci; a sauya tsarin makarantun allo, kana ake bayar da karatun addini dai dai da dacewa.

Da aka tambaye shi akan yunƙurin da gwamnatoci keyi don magance matsalar ya ce; "gwamnati bata yin wani abin azo a gani, sun kasa yin kataɓus akan matsalar.

"A baya an sha kawo tsarin ilmintar da makiyaya amma da zarar wanda ya kawo tsarin ya bar gwamnati ko ya sauka daga karagar mulki to fa shikenan tsarin ya sha ruwa, labarin zai sha ban-ban, ba zaka sake jin ɗuriyar batun ba, kamar yadda ya faru a baya lokacin gwamnatin Babangida."

Ana tsammanin mulki zai koma kudancin ƙasar nan a shekarar 2023. A matsayinka ɓa fitaccen ɗan siyasa kuma malamin addinin musulunci,kana tsammani mulki ya ke juyawa bisa yanki ko kuwa bisa addini saboda a samu wakilcin da ya dace?

"Idan har aka shigo da batun addini cikin ababen dubawa wajen bada mulki, to ba shakka sai an samu tangarɗa da matsala, amma magana ta gaskiya, ba zamu iya gujewa hakan ba.

"Alal misali, bayan shekaru takwas Musulmi ɗan arewa yana mulkar ƙasa, zai fi dacewa ɗan kudu Kirista ya karɓi mulki.

"Musulmi ɗan kudu zai iya samu mulki ne kawai idan har mutanen kudu maso kudu, kudu maso gabas, kudu maso yamma da ƴan tsakiyar Najeriya zasu yarda kuma su amince ba tare da sun lazimci addininsu ko imanin su ba.

"Abin da ba zamu taɓa laminta ba a arewa shine musulmi ɗan kudu ya ɗauko Kirista ɗan arewa a matsayin mataimakinsa na shugaban ƙasa."

Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa gwamnonin jam'iyyar APC sun yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, da yammacin ranar Juma'a a Abuja.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng