Atiku ya fadi daliin da yasa tattalin arzikin Nigeria ke karyewa a karkashin mulkin Buhari

Atiku ya fadi daliin da yasa tattalin arzikin Nigeria ke karyewa a karkashin mulkin Buhari

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce ya matukar girgiza da samun labarin cewa tattalin arzikin Nigeria ya sake karyewa

- Wannan shine karo na uku da tattalin arzikin Nigeria ya sake karyewa a karkashin mulkin Buhari

- Atiku ya ce lokaci ya yi da ya kamata shugaba Buhari ya bude kunnuwansa ya ajiye siyasa a gefe, ya saurari shawarwarinsu

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya wallafa sakon shawarwari ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bayan tattalin arzikin Nigeria ya sake karyewa a karo na uku.

"Zuciyata ta yi nauyi sakamakon samun tabbacin mun sake faɗawa ruwa a karo na biyu sanadiyyar mashasharar tattalin arziƙi, Najeriya ta sake faɗawa ƙangin tattalin arziki.

"Eh, tabbas annobar COVID-19 ita ce silar janyo wannan matsala, sai dai, da tuni mun kaucewa wannan hali ta hanyar ta amfani da basira gami da hangen nesa tare da tattala tattalin arziƙin mu.

"Tunda mai afkuwa ta afku, ba haƙƙin kowa bane tada jijiyar wuya akan batun. Dole mu maida hankulanmu kan nemo mafita. Najeriya na buƙatar nagartaccen shugabancin da zai ja akalarta zuwa hanyar farfaɗo da tattalin arziƙinmu.

KARANTA: Ekiti: An shiga har cikin Caji Ofis an harbe dan sanda a babban Ofishinsu da ke Ado

"Ba zai yiwu mu naɗe hannayen muyi zuru ba. Dole mu ɗauki mataki ta hanyar gudanar da abubuwan da suka zama dole, wataƙila matakan su kasance masu zafi da raɗaɗi.

Atiku ya fadi daliin da yasa tattalin arzikin Nigeria ke karyewa a karkashin mulkin Buhari
Atiku ya fadi daliin da yasa tattalin arzikin Nigeria ke karyewa a karkashin mulkin Buhari
Asali: Twitter

"Farawa da kasafin kuɗin da aka gabatarwa majalisa a ranar Talata, 8 ga watan Oktoba 2020, baya cikin tsari yanzu.

"Najeriya ba tada ma'adanai ko buƙatar kasafin alatu mai tsada irin wanda shugaban kasa ya gabatar.

"Ƙasa ta tagayyara, amma bata rushe ba. Duk da haka, idan muka cigaba da almubazzaranci, ko da abin da muke samu bai kai gejin da muke nema ba, ƙasar zata tashi daga tagayyararriya zuwa rusashiyar ko ɓallaliyar ƙasa.

KARANTA: 2023: Ba zamu taba lamunta a dauki Kirista daga arewa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa ba; Jigo a APC, Fafresa Mahuta

"Saboda kaucewa hakan, akwai matakan da ya kamata gwamnati ta dauka cikin gaggawa.

"Wannan ya haɗar da soke tafiyar da ba ta gaggawa da hanzari ba, rage kudin ciyarwar shugabanni, hakura bushasha da jindaɗi, dakatar fita horo a ƙasashen waje, hakura da siyo sabbin ababen hawa da gyaran ofisoshi da kuma alawus ɗin da bana albashi ba da sauransu," kamar yadda Atiku ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Atiku ya ce lokaci ya yi da ya kamata shugaba Buhari ya bude kunnuwansa, ya saurari shawarwarin da ake bashi a kan hanyoyoyin gyara tattalin arzikin Nigeria ba tare da la'akari da banbancin jam'iyya ba.

A baya Legit.ng Hausa ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta gama kammala tsare tsare don ganin ta zabge harajin motocin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje daga kaso 35% zuwa kaso 30%.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel