'Yan bindiga sun sace manyan jami'ai 8 daga tawagar 'yan sanda

'Yan bindiga sun sace manyan jami'ai 8 daga tawagar 'yan sanda

- Lauya mai rajin kare hakkin bil'adama, Bulama Bukarti, ya yi tsokaci a kan rahoton da BBC Hausa ta wallafa.

- A ranar Talata ne BBC Hausa ta rawaito cewa 'yan bindiga sun sace manyan jami'an 'yan sanda har goma sha biyu a tsakanin jihar Katsina da Zamfara

- Labarin sace 'yan sandan bai bayyana ba sai yanzu, bayan kwana goma, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito

BBC Hausa sun kawo rahoton cewa ƴan bindiga sun ƙwamushe ƴansanda goma sha biyu dukkaninsu masu muƙamin ASP.

A cewar BBC Hausa, an sace 'yan sandan ne kwanaki goma da suka gabata bayan 'yan bindiga sun kai wa tawagarsu harin kwanton bauna.

Matar ɗaya daga cikin jami'an ƴansandan ita ce wadda ta shaidawa BBC cewa mijinta ya umarceta da ta siyar da gidan da suke zaune don samun kuɗin fansa. Ta ce ta san iyalan sauran jami'ai takwas da aka sace su tare da mijinta.

KARANTA: Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Katsina, sun kashe na kashewa, sun kwaci makamai da dukiya

Iyalan jami'an suna ta faman ƙoƙarin haɗa ₦800,000 kowannensu don biyan kuɗin fansa.

Lokacin da BBC ta tuntuɓi rundunar ƴansanda reshen jihar Borno, tunda daga nan ne aka tura jami'an, sai suka ce su tuntuɓi rundunar reshen jihar Zamfara ko Katsina.

Sai dai gaba ɗayansu wato rundunar jihar Borno, Zamfara da Katsina sun ce basu da wata masaniya dagane da lamarin.

'Yan bindiga sun sace manyan jami'ai 8 daga tawagar 'yan sanda
'Yan bindiga sun sace manyan jami'ai 8 daga tawagar 'yan sanda
Asali: UGC

Lauya mai rajin kare hakkin bil'adama, Bulama Bukarti, ya ce; "abun fargaba ne da razani yadda al-amura ke ƙara ta'azzara a yankin arewa maso yammacin ƙasar nan.

KARANTA: Bayan sun sace mana shanu, yanzu kuma sai mun biya N1m kafin mu girbi amfanin gona - Manomin shinkafa a Zamfara

"Idan har za'a iya ƙwamushe jami'an ƴansanda cikin ayari, to me kuma ya rage, ina makomar sauran karabitin mutane dake zaune kara zube ba tare da makami ko horon kare kansu ba?

"Abune a bayyane, haƙiƙa muna wasa da wuta wadda nan gaba zata ƙona mu in har muka yi sake."

A ranar Litinin ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa kwamanda a rundunar soji ya yanke jiki ya fadi matacce yayin da ya ke tsaka da gabatar jawabi ga sojoji a wurin bayar da horon yaki da ta'addanci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng