Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Katsina, sun kashe na kashewa, sun kwaci makamai da dukiya

Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Katsina, sun kashe na kashewa, sun kwaci makamai da dukiya

- Rundunar sojin Najeriya sun yi gagarumin nasara a kan yan bindiga a Katsina

- Sojoji sun ragargaji 'yan bindigan, sun kawar da wasu da dama sannan sun kwato makamai

- Hakan na daga cikin kokarin da suke na kawar da ta'addanci da sauran muggan laifuka a arewa maso yamma

Jami'an atisayen ACCORD sun kawar da wasu ƴan bindiga daɗi,sun kama wasu da ake zargi da kuma sun kwace makamai a Jihar Katsina.

Acigaba da ake na atisayen kawar da ta'addanci da sauran muggan laifuka a arewa maso yamma na ƙasar Najeriya,jami'an atisayen ACCORD sun sami gagurumar nasara.

Jami'an Atisayen ACCORD a ranar 15 ga watan Nuwamba 2020 lokacin wani sumamen dare a ƙauyen Ƴar Tasha sun yi kiciɓus da ƴan bindiga daɗi inda akayi musayar wuta.

Lokacin musayar wutar,an sheƙe uku daga cikin ƴan bindiga daɗi,inda wasu daga cikinsu suka tsere da munanan raunuka sanadiyyar harbin bindiga.

KU KARANTA KUMA: Addinin musulunci ya samu babban karuwa: Fastoci fiye da 42 da matayensu sun musulunta a Abuja (hotuna)

Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Katsina, sun kashe na kashewa, sun kwaci makamai da dukiya
Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Katsina, sun kashe na kashewa, sun kwaci makamai da dukiya @Thecable
Asali: Twitter

An samu nasar ƙwace bindigu ƙirar AK 47 guda 3 lokacin da akayi musayar wuta daga hannun miyagun.

A wani cigaban kuma,bayan samun bayanan sirri akan motsin ƴan bindiga daɗin,sojoji sun gudanar da sumamen farmaki tsakanin ƙauyukan Natsinta da Dawanna a ƙaramar hukumar Jibia tsakanin titin Katsina zuwa Jibia.

A wannan atisayen,sojoji sunyi nasarar daƙume ƴan bindiga daɗi guda 10,lokacin da suke ƙoƙarin yin hijira tare da dabbobin da suka kwace.

Lokacin da ake tuhumar su,bayan da gyaɗa taji matsa,bakwai (7) daga cikinsu sunce sunyo hijira ne daga ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara zuwa jamhuriyyar Nijar.

An kama waɗanda ake zargin da shanu 88 da tumaki wanda ba'a gano adadinsu ba.Yanzu haka waɗanda ake zargin suna hannun hukuma ana cigaba da gudanar da bincike.

Hakazalika,sojojin da aka kai Unguwan Doka a ranar 15 ga watan Nuwamba 2020,sun ceto wani mutum da aka sace mai suna Adamu Yahaya.

KU KARANTA KUMA: Ilimin ƴaƴa mata: Hankalin Sarakunan Arewa ya tashi kan wasu jihohi 5

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa an ƙwamushe mutumin ne a Unguwar Sa'ida,wani ƙauye a ƙaramar hukumar Faskari.

Tuni aka miƙa wanda aka ceto gun iyalansu. Yanzu haka, sojoji suna cigaba da mamaye yankin ta hanyar kai sumame akai-akai don samar da tsaro da kuma hana ƴan bindiga samun sukunin kai hare-hare.

Rundunar sojin ta yabawa ƙoƙarin jami'anta bisa nuna ƙwarewa a aikinsa,sun kuma ƙarfafa musu guiwa kan su cigaba da dukkan wani yunƙuri don kawar da dukkan wata barazanar tsaro da masu aikita munanan laifuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng