Bayan sun sace mana shanu, yanzu kuma sai mun biya N1m kafin mu girbi amfanin gona - Manomin shinkafa

Bayan sun sace mana shanu, yanzu kuma sai mun biya N1m kafin mu girbi amfanin gona - Manomin shinkafa

- Rahotanni sun sha kawo yadda 'yan bindiga dadi ke cin karensu babu babbaka a kauyukan jihar Zamfara

- Mazauna sassan jihar sun sanar da manema labarai cewa 'yan binduga sun saka musu haraji a kan noman da suka yi lokacin damuna

- Hakan na nufin manomi ba zai girbi amfanin gonarsa ba sai ya biya kudin da 'yan bindigar da suka yanka masa

Ƴan bindiga su na cigaba da sace mana dabbobi, baya ga karɓar kuɗin fansa akan ƴan'uwan mu da suka sace, yanzu haka kuma sai mun biya harajin noma a gonakinmu kafin mu girbe amfani.

Wani babban manomin shinkafa a jihar Zamfara, Alhaji Nuhu Deme, ya bayyana irin halin tsaka mai wuyar da suke ciki a Zamfara, yayin hira da wani gidan rediyo MAIHARAJI ALTINE, akan yadda ƴan bindiga suka saka manoma wahala a jihar.

Ya ce duk da irin yabanyar da aka samu a daminar bana, musamman a arewacin ƙasar nan duba ga yadda aka samu amfani mai ɗimbin yawa sanadiyyar wadatuwar ruwan sama.

KARANTA: Kwamandan rundunar Soji ya yanke jiki ya faɗi matacce ana tsakiyar horon yaƙi da Boko Haram

A wurinsu hakan bai yi wani alfanu ba sakamakon ayyukan ƴan bindiga a yankin Zamfara.

"Ƴan bindiga suna mamaye gonakinmu kuma sun yi iyakar ƙoƙarinsu don ganin bamu sami wata riba ko alfanu ba.

Bayan sun sace mana shanu, yanzu kuma sun biya N1m kafin mu girbi amfanin gona - Manomin shinkafa
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara @Daily_nigerian
Asali: Twitter

"Abin da nake nufi shine ƴan bindiga ɗauke da makamai suna bin gonakinmu suna sa ido don su tabbatar babu wanda ya girbe amfanin gonarsa har sai ya biya harajin da suka yanke masa.

A maganar da nake maka, yanzu haka tuni wasu manoman sun biya harajin da suka yanke musu."

Da aka tambaye shi akan nawa suke karɓa duk gona sai yace; "ya danganta da irin girma da kuma adadin abin da aka shuka a gonar.

"Harajin ya na farawa daga Naira dubu ɗari zuwa miliyan ɗaya (₦100,00-₦1m) kuma dole sai an biya waɗannan kuɗaɗen kafin a samu a girbe amfanin gonar.

KARANTA: Saurayi ya kashe mahaifiyarsa saboda zaman dadiro da saurayi a gidansu

"Idan kuma mutum bazai iya biya ba saboda halin rashin kuɗi ko babu, sai ka girbe amfanin tsaf sai su ɗibi na ɗiba su bar maka sauran.

"Idan kuma manomi yaƙi bin umarninsu, ko dai su saki shanu su cinye, su lalata amfanin gonar ko kuma su ƙwamushe manomin idan yazo girbar amfanin gonarsa. Da yawa daga cikin mutane sun faɗa tarkon ayyukan sheɗancin ƴan bindigar.

"Wata hanyar daban ta karɓar haraji daga hannu manoman shine ta hanyar buƙatar kuɗi daga mutanen ƙauyen. Za su turo saƙo suce mutanen ƙauye su biya wasu kuɗaɗe idan suna son girbe amfaninsu ba tare da katangewa ba.

Zasu ce ƙauyuka su biya haraji dai-dai gwargwadon ƙarfin arziƙin al-ummar su. Wasu daga cikin ƙauyuka anan masaurautar Ɗansadau a ƙaramar hukumar Maru suna biyan tsakanin ₦500,000 zuwa miliyan ɗaya ₦1m kuma da yawa sun biya."

A makonda ya gabata ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa, gwamnatin Zamfara ta sanar da kubutar da wasu 'yammata 26 da 'yan bindiga suka sace tare da yin garkuwa da su a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng