Kwamandan Sojojin Najeriya ya yanke jiki ya faɗi,Ya mutu ana tsakiyar horon yaƙi da ta'addanci

Kwamandan Sojojin Najeriya ya yanke jiki ya faɗi,Ya mutu ana tsakiyar horon yaƙi da ta'addanci

- Kwamanda a rundunar soji ya yanke jiki ya fadi matacce yayin da ya ke tsaka da gabatar jawabi ga sojoji

- Kakakin rundunar soji bai samu damar amsa kiran jaridar Gazette don jin inda aka tsaya dangane da sababin mutuwar babban sojan ba

- 'Yan Najeriya na cigaba da nuna fushi da bacin ransu a kan yadda yakin Boko Haram ke cigaba da zama silar asarar rayukan jami'an tsaro da fararen hula

Wani Kwamandan soji ya yanke jiki ya faɗi lokacin da ake bada horon yaƙi da ta'addanci,kuma ya rasu jim kaɗan bayan an garzaya dashi asibiti a Maiduguri, kamar yadda jaridar Peoples Gazette ta rawaito.

Laftanar Kanal Isah Yusuf, kwamandan bataliya ta 158 Task force, ya yanke jiki ya fadi da misalin ƙarfe takwas da arba'in 8:40 na safiyar ranar Asabar a daidai lokacin da ya ke yi wa sojoji jawabi a wani ɓangare na bada horon yau da kullum don yaƙar ta'addancin Boko Haram, a cewar majiyarmu.

DUBA WANNAN: Sabuwar doka: Ma su digiri mai daraja ta farko da ta 2:1 kadai za'a bawa aikin koyarwa; FG

Ya rasu da misalin ƙarfe tara da arba'in da biyar 9:45a.m ranar Asabar a asibitin sojoji rundunar sojin Najeriya na 7 Division da ke Maiduguri, majiya daga rundunar soji ta faɗi hakan cikin ɓacin rai da alhini ga jaridar Gazette. Har yanzu ba'a kai ga tantance asalin sababin mutuwarsa ba.

Kwamandan Sojojin Najeriya ya yanke jiki ya faɗi,Ya mutu ana tsakiyar horon yaƙi da ta'addanci
Kwamandan Sojojin Najeriya ya yanke jiki ya faɗi,Ya mutu ana tsakiyar horon yaƙi da ta'addanci @Premiumtimes
Asali: Twitter

Mai magana da yawun rundunar soji yaƙi amsa kira daga jaridar Gazette don jin inda aka tsaya a yammacin ranar Asabar.

DUBA WANNAN: Saurayi ya bankawa kansa da budurwarsa wuta bayan ya malale dakinsu da fetur

Jaridar The Gazette ta gano cewar Hedikwatar soji sun turawa iyalan mamacin saƙon kar ta kwana, sun sanar da su afkuwar lamarin, kafin suzo daga bisani don tura wakilai a hukumance don sanar da iyalan mamacin.

Ƴan Najeriya na cikin fushi sakamakon ayyukan ta'addancin Boko Haram dake cigaba da salwantar da rayukan manya da ƙananan sojoji da sauran al-umma,duk da alƙawuran da hukumomin tsaro da ƴan siyasa keyi na cewar ana gaɓar ƙarshe na kawo ƙarshen yaƙin.

Rundunar soji, a ranar Asabar, ta musanta zargin yin amfani da harsashin gaske a kan fararen hula da suka yi dandazo a Lekki, jihar Legas, yayin da suke gudanar da zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS; wato ENDSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng