Zan fanshi 35% na hannun jarin kungiyar kwallon Arsenal inji Sanata Kalu

Zan fanshi 35% na hannun jarin kungiyar kwallon Arsenal inji Sanata Kalu

- Orji Uzor Kalu mai wakiltar Abia a Majalisa ya na son zuba jari a Arsenal

- Tsohon Gwamnan jihar Abia ya ce zai saye 35% na hannun jarin kungiyar

- Kalu ya bi sahun Aliko Dangote da ya ke da burin fansar kungiyar kwallon

Orji Uzor Kalu, Sanatan da ke wakiltar arewacin jihar Abia a majalisar dattawa ya kudiri niyyar sayen kashi 35% na hannun jarin kungiyar Arsenal.

Sanata Orji Uzor Kalu ya yi gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007, ya ce yanzu burinsa shi ne ya zuba jari a kungiyar ta yadda za ta kai ga samun nasarori.

A tarihi, kungiyar kwallon kafan Arsenal ba ta taba samun nasarar cin gasar ‘Champions League’ ba, Kalu ya na sa rai zai kai kungiyar ga wannan nasara.

KU KARANTA: Hotunan katafaren gidan Aliko Dangote

Uzor Kalu ya bayyana cewa ya na da burin ganin Arsenal ta lashe gasar Firimiya sau biyu a jere. Abin da kungiyar Ingilar ta shafe shekaru ba ta yi ba.

A lokacin da ya ke gwamna a Abia, kungiyar kwallon Enyimba da ke garin Aba ta lashe gasar Firimiyan Najeriya a 2001, 2002, 2003, 2005 da 2007.

“Nasarar da mu ka samu da kungiyar kwallon kafan Enyima tsakanin 2000 da 2007, ya kara mani sha’awar wasan kwallon kafa.” Inji Orji Uzor Kalu.

Sanatan ya ce a Facebook: “A matsayina na jigon wasanni a Afrika, ina tunanin zuba kudi a harkar kwallo, don haka zan saye 35% na kungiyar Arsenal.”

KU KARANTA: Za a samu Miliniyoyi 60 a tsarin garabasar Kamfanin Dangote

Zan fanshi 35% na hannun jarin kungiyar kwallon Arsenal inji Sanata Kalu
Sanata Orji Uzor Kalu Hoto: Mujallar Interview
Asali: Depositphotos

“Burinmu shi ne mu dauki kofin Champions League da Firimiya sau biyu a jere, kamar yadda mu ka yi da Enyimba.”

Kafin ‘dan siyasar, tun ba yau ba, mai kudin Najeriya da nahiyar Afrika, Aliko Dangote ya shaida wa Duniya cewa zai nemi sayen kungiyar Arsenal.

A ranar Litinin ku ka ji cewa tsohon Tauraron Super Eagles, Christian Obodo, ya sake shiga hannun Miyagu. Amma ‘yan bindigan sun saki 'dan wasan.

A 2012 an taba yin garkuwa da Obodo har sai da aka biya wasu kudi da ake zargin masu yawa ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel