Aljannar duniya: Hotunan cikin katafaren gidan attajiri, Aliko Dangote

Aljannar duniya: Hotunan cikin katafaren gidan attajiri, Aliko Dangote

Aliko Dangote shine bakin mutum mafi kudi a duniya a yau. Ba abun mamaki bane idan aka ce yana rayuwa a gidan da za a kira da 'aljannar duniya'. Rade-radi sun bayyana cewa, gidan Aliko Dangote ya kai darajar $30million. Gidan na nan a Abuja. Zata yuwu gidan ne gida mafi kyau da mai karatu ya taba gani.

Daga wajen gidan, anyi masa fenti da farin gilashi inda aka yi masa yarfi a jiki duk da tagogin. Katangar gidan da ke zagaye da daular duniyar itama tana da fenti fari ne. Kofar gidan wani katon bakin kyaure ne wanda ya tsaru saboda farin fenti dake kewaye da gidan. Harabar gidan kuwa a tsaftace take a koda yaushe kuma ta kawatu da ciyawa launin kore.

Aljanar duniya: Hotunan cikin katafaren gidan attajiri, Aliko Dangote
Gidan Aliko Dangote ta gaba
Asali: Twitter

A ta cikin gidan kuwa, an tsara ne da wasu irin kayan kawa na 'Victorian Beauty'. A takaice dai, kowanne daki dake cikin gidan nan ya tsaru. Akwai katon daki wanda aka kawata shi da manyan kujeru da kuma wasu irin kayan haske tare da fenti mai matukar kawatar da wanda ke kallo.

Aljanar duniya: Hotunan cikin katafaren gidan attajiri, Aliko Dangote
Gidan Aliko Dangote
Asali: Instagram

DUBA WANNAN: Soyayya: Ahmed Indimi da Zahra Buhari sun yi murnar cikar shekara uku da aure (Hotuna)

Kamar yadda rade-radi ke nunawa, wannan shine dakin da Dangote ke amfani dashi matukar zai yi taronsa na kasuwanci ko wata tattaunawa da jami'an gwamnati ko abokan kasuwanci.

Madafin gidan kuwa, wani abun kallo ne na daban kamar a aljanna. Haske da yanayin tsarin madafin kuwa, ba abu ne da mai karatu zai iya kintatawa ba. Da yawa daga cikin otal din Najeriya, ba a samun kamarsa.

Aljanar duniya: Hotunan cikin katafaren gidan attajiri, Aliko Dangote
Kitchen
Asali: Instagram

Akwai wani katon talabijin da ke sagale a daya daga cikin ginshikan madafin. Wajen ajiye-ajiye na madafin kuwa duniya ce ta daban. Akwai kujerun da mutum zai iya zama a kusa dasu.

Dakunan baccin wannan gida kuwa ba abu ne da mai karatu zai iya fahimta ba matukar bai ga hoton ba ko kuma ya je da kansa.

Aljanar duniya: Hotunan cikin katafaren gidan attajiri, Aliko Dangote
Dakin bacci
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng