Za a samu Miliniyoyi 60 a dalilin tsarin garabasar Kamfanin simintin Dangote

Za a samu Miliniyoyi 60 a dalilin tsarin garabasar Kamfanin simintin Dangote

Shirin garabasar da kamfanin simintin Dangote ya kawo zai yi sanadiyyar samar da mutane akalla 60 da za su ci kyautar Naira miliyan daya.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 17 ga watan Agusta cewa sabon shirin Goodies Promo na kamfanin Dangote ya na cigaba taimakawa mutane.

A wannan zango na tsarin garabasar kamfanin Dangote, ana neman samar da masu kudi 60 a jihohin kasar nan, kamfanin ya na wannan ne domin rage radadin COVID-19.

Annobar cutar COVID-19 da ta addabi ta karya tattalin arzikin mutane da kasashe, wannan ya sa kamfanin Dangote Cement ya sake kawo wannan tsari a Najeriya.

Shugabar harkar kasuwanci da kamfanin, Misis Funmi Sanni, ta shaida cewa duk da mutanen su ka yi dace, akwai karin wadanda za su samu gawurtattun kyaututtuka.

A wajen gabatar da kyatuttuka ga wadanda su ka yi nasara, Funmi Sanni ta ce mutane 27 sun taki babbar sa'a, kuma kudinsu sun shigo masu a makon da ya gabata.

KU KARANTA: Attajirai 8 da su ka sha gaban kowa a Nahiyar Afrika

Za a samu Miliniyoyi 60 a dalilin tsarin garabasar Kamfanin simintin Dangote
Aliko Dangote mai kamfanin Dangote
Asali: UGC

A cewar darektar, masu ciniki a kamfanin Dangote za su iya samun kyauta har ta Naira miliyan daya bayan sun karbi wasu kati da ke dauke da wasu jerin harufa.

Duk wanda ya yi dacen cinko harufan D, A, N, G, O, T da E, ya hada sunan DANGOTE, zai tashi da wasu daga cikin jeringiyar kyaututtukan da ake rabawa a Birane.

Rahoton ya ce irin kyaututtukan da ake samu daga kamfanin simintin na Dangote sun hada da babur, keke napep, akwatin talabijin, katin wayar salula da dai sauransu.

Za a rufe wannan garabasa ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2020 inji kamfanin.

Wani babban jami’in kamfanin Dangote, Rabiu Umar, ya ce sun kawo wannan shiri ne domin agazawa mutane a sakamakon annobar COVID-19 da ta rutsa da Bayin Allah.

Umar ya ce kamfanin Dangote zai rabawa mutum 1000 kyautar Naira Biliyan daya. Ya ce: “Mu na ganin cewa duk da annobar nan, ya kamata mu sa masu ciniki da mu farin ciki.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel