Delta: Christian Obodo ya fada hannun Masu garkuwa da mutane, ya fito
- Tsohon Tauraron Super Eagles, Christian Obodo, ya sake shiga hannun Miyagu
- Da ya ke akwai sauran kwana a gaba, ‘Yan bindigan sun saki wannan Mutumi
- An taba yin garkuwa da Obodo a shekarun baya har sai da aka biya wasu kudi
Tsohon ‘dan wasan kwallon kafan Najeriya, Christian Obodo, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, 2020, ya fito.
The Nation ta fitar da rahoto cewa Christian Obodo ya samu ‘yanci a ranar Lahadi da daddare. Ba mu da labarin ko ya biya kudin fansa ko bai biya ba.
Kamar yadda rahotanni su ka zo, an sace Obodo ne a hanyar zuwa matatar mai da ke garin Effurun, da ke karamar hukumar Uvwie, a jihar Delta.
Jaridar ta tabbatar da fitowar wannan Bawan Allah daga hannun masu garkuwa da mutane dazu.
KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun dawo titin Abuja, sun yi garkuwa da mutane
Wani abokin tsohon ‘dan kwallon, Big Sam ya shaida wa ‘yan jarida cewa: “An fito da shi. An fito da shi ne jiya. Na hadu da shi yau da safe.”
“Garin nan ya na kara zama abin tsoro. Mu na murna da ya dawo gida.” Inji Injiniya Big Sam.
Tsohon ‘dan wasan na Udinese ya fada tarkon masu garkuwa da mutanen ne yayin da ya tsaya a kan hanya domin ya saye ayaba a garin Effurun.
Ba wannan ne karon farko da aka taba sace tsohon tauraron Duniyan ba, a watan Yunin 2012, an sace shi a lokacin da ya ke hanyarsa ta zuwa coci.
KU KARANTA: 'Yan Sanda su na binciken Kocin kasar Wales, Ryan Giggs
Obodo mai shekara 36 a Duniya ya yi ritaya daga buga kwallo ne a kungiyar Appollon Smyrnis. Sai da aka biya kudi kafin a karbi fansarsa kwanaki.
Da aka tuntubi jami’an tsaro sun nuna ba su da masaniya game da lamarin kamar yadda kakakin ‘yan sandan Delta, Onome Onovwakpoyeya, ya fada.
Gwamnatin Kano ta amince da nada Bafaranshen a matsayin Kocin kungiyar kwallon kafan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng