Garƙame asusun bankuna: Ana shirin fara sabuwar zanga zangar #EndSARS

Garƙame asusun bankuna: Ana shirin fara sabuwar zanga zangar #EndSARS

- Akwai fargabar cewa ana shirin fara sabuwar zanga-zangar EndSARS bayan CBN ya sami yardar kotu don daskarar da asusun wasu masu zanga-zanga

- Kotun ta ba CBN izinin daskarar da asusun har zuwa lokacin da za ta kammala bincikenta

- Tuni lamarin ya kawo tsaiko a harkokin kwamitin shari’a na Lagas yayinda umurnin kotun ya shafi daya daga cikin wakilan matasa da ke kwamitin

Wani rahoto daga jaridar The Nation ya nuna cewa akwai barazana na fara sabuwar zanga-zangar #EndSARS wanda bata gari suka kwace a baya.

A cewar rahoton, sabon ci gaban zai kasance ne sakamakon daskarar da asusun wasu shahararrun matasa da suka gudanar da zanga-zangar #EndSARS da aka yi.

An tattaro cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sami umurnin kotu don daskarar da asusun mutane da kungiyoyi 20 wadanda ke da nasaba da zanga-zangar ta #EndSARS.

KU KARANTA KUMA: Ka gaggauta yin zaɓen shuwagabannin APC ko ka sauka daga riƙon ƙwarya - Marafa ga Buni

Garƙame asusun bankuna: Ana shirin fara sabuwar zanga zangar #EndSARS
Garƙame asusun bankuna: Ana shirin fara sabuwar zanga zangar #EndSARS Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Umurnin kotun ya shafi daya daga cikin wakilan matasa a kwamitin shari’a ta Lagas, Rinu Oduala.

Hakan, ya yi sanadiyar dage zaman kwamitin yayinda wakilan matasan suka kauracewa zaman a ranar Asabar, 7 ga watan Nuwamba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa yan Najeriya da dama musamman matasa sun je shafukan soshiyal midiya domin yin Allah-wadai da yunkurin babban bankin kasar, cewa hakan na iya haifar da sabuwar zanga-zanga.

KU KARANTA KUMA: Kariya zamu bata: Dalilin da ya sa rundunar ƴan sanda ta gayyaci Rahama Sadau

An tattaro cewa kotun ta umurci bankuna da su daskarar da dukkanin harkoki a asusun bankunan masu zanga-zangar na #EndSARS da abun ya shafa har na tsawon kwanaki 180 zuwa lokacin da za a samu sakamakon binciken da CBN ke gudanarwa a yanzu.

A gefe guda, kwamitin bincike kan barnar da aka yi wa rundunar yan sandan Najeriya a yayin zanga-zangar neman a rushe rundunar tsaro na SARS, ya bayyana cewa an sace bindigogin AK-47 kimanin guda 100 a Lagas.

Shugaban rundunar yan sandan kasar, Mohammed Adamu ne ya kafa rundunar don yin wannan aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng