Kariya zamu bata: Dalilin da ya sa rundunar ƴan sanda ta gayyaci Rahama Sadau

Kariya zamu bata: Dalilin da ya sa rundunar ƴan sanda ta gayyaci Rahama Sadau

- Wata majiya ta tsaro ta bayyana dalilin da yasa rundunar yan sanda ta gayyaci Rahama Sadau

- Majiyar ta ce kariya rundunar ke son ba jarumar domin hana karya doka

- An ta samun cecekuce tun bayan wallafa wasu hotuna da Rahama ta yi a shafukanta

Rahotanni sun kawo cewa wani babban majiyi na yan sanda ya bayyana cewa rundunar yan sandan Najeriya bata da niyar kama jarumar Kannywood, Rahama Sadau.

Majiyin ya bayyana cewa gayyatar da hukumar yan sandan ta yi wa jarumar domin bata kariya ne da kuma hana karya doka a jihar Kaduna, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Babban jami’in dan sandan ya tabbatar da cewa Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu ya rubuta wata wasika zuwa ga kwamishinan yan sandan Kaduna, Umaru Muri, inda ya umurce shi da ya yi bincike a kan lamarin da ya kai ga zargin batanci ga Annabi.

Ya ce an gano inda Rahama ta koma tare da iyayenta a Abuja bisa tsoron cewa ana iya cutar da ita sannan aka tura wata tawagar jami’an yan sanda domin su dawo da ita Kaduna don amsa tambayoyi.

KU KARANTA KUMA: Nasara ta samu: Rundunar ƴan sanda ta yi holen manyan ƴan fashi 4 a Katsina

Majiyin wanda yace ba a bashi izinin yin magana ba ya ce tawagar yan sabdan sun dawo Kaduna a ranar Asabar ba tare da Rahama ba.

Kariya zamu bata: Dalilin da ya sa rundunar ƴan sanda ta gayyaci Rahama Sadau
Kariya zamu bata: Dalilin da ya sa rundunar ƴan sanda ta gayyaci Rahama Sadau Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Babu wani umurni na cewa a kama ta, mun samu korafe-korafe fa dama a kanta kuma idan kuka duba wasikar IG, kawai ya umurci CP din ne da ya tabbatar da cewa lamarin bai zama barazana ga kwanciyar hankalin jama’a ba, saboda haka mun so ji daga gareta ne da kuma fahimtar irin barazanar da take ya samu,” in ji shi.

An dai ta yi cece-kuce a kan jarumar tun bayan bayyanar wani hoto da ta wallafa a shafukanta na sadarwa.

Sai dai ba a ji ta bakin kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Saboda gaza ɗaukar ɗawainiya: Kotu ta warware auren shekaru 7

A baya mun ji cewa Jarumar Kannywood wacce aka fi sani da Fati Slow-motion ta mayar da martani ga Mansura Isa a kan fallasar da ta yi wa yan matan Kannywood da suka caccaki Rahama Sadau kan shigar da tayi.

Fati ta gargadi Mansura a kan ta kiyaye ta don kada ta bari su yi tone-tone, idan ba haka ba sai ta kwance mata zani a kasuwa.

Ta kuma shawarceta da ta je ta rungumi aurenta maimakon ganinta da ake yi a tsakiyar maza a koda yaushe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel