Sakamakon zanga zangar #EndSARS: Yan daba sun saci bindigar AK-47 guda 100 a Legas

Sakamakon zanga zangar #EndSARS: Yan daba sun saci bindigar AK-47 guda 100 a Legas

- Kwamitin shugaban yan sandan Najeriya kan barnar da aka yi a lokacin zanga-zangar EndSARS ta fara fitar da bayanai

- Kwamitin wanda CP Yaro Abutu ke jagoranta, ya ce yan daba sun sace bindigogin AK-47 kimanin guda 100 a Lagas

- Abutu ya nuna rashin jin dadinsa ganin cewa wannan barna na zuwa ne a lokacin da aka fi yin ta'asa a kasar wato a karshen shekara

Kwamitin bincike kan barnar da aka yi wa rundunar yan sandan Najeriya a yayin zanga-zangar neman a rushe rundunar tsaro na SARS, ya bayyana cewa an sace bindigogin AK-47 kimanin guda 100 a Lagas.

Shugaban rundunar yan sandan kasar, Mohammed Adamu ne ya kafa rundunar don yin wannan aiki.

Shugaban kwamitin mai mamba 10, CP Yaro Abutu, ya bayyana cewa baya ga bindiogin, an kuma yi awon gaba da harsasai guda 2,600 duk a yayin rikicin zanga-zangar EndSARS.

KU KARANTA KUMA: Nasara ta samu: Rundunar ƴan sanda ta yi holen manyan ƴan fashi 4 a Katsina

Sakamakon zanga zangar #EndSARS: Yan daba sun saci bindigar AK-47 guda 100 a Legas
Sakamakon zanga zangar #EndSARS: Yan daba sun saci bindigar AK-47 guda 100 a Legas Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Hakazalika ya bayyana cewa an kai hari tare da lalata wuraren 'yan sanda guda 37 a jihar. Sannan kuma, an lalata ababen hawansu guda 367, ciki har da motar silke 10 da kuma kanana da kirar Hilux na fita fatro.

Ya kuma bayyana cewa suna nan suna tattara asarar da 'yan sandan suka yi a fadin kasar baki daya.

A bisa rahoton jaridar Punch, ta ce kwamitin zai mika rahotonsa ga Sufeto Janar na yan sanda a nan da makonni uku.

Abutu ya koka cewa "abin takaici ne yadda aka aikata ta'asar a karshen shekara, lokacin da aka fi aikata laifuka a fadin kasar".

KU KARANTA KUMA: Saboda gaza ɗaukar ɗawainiya: Kotu ta warware auren shekaru 7

"Muna duba abubuwan da suka faru a jiha 17 da aka kona ofisoshi da kuma kisan 'yan sanda. Tun da Legas ce cibiyar zanga-zangar, shi ne muka yanke shawarar fara zuwa nan.

"Ofishin 'yan sanda 37 aka kai wa hari a Legas kuma an gurgunta kusan kashi 30 cikin 100 na ayyukan 'yan sandan a jihar."

A wani labarin, mun ji cewa rashin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro yasa mutane sun shiga tsaka mai wuya a titunan Najeriya, inda 'yan ta'adda suka samu dama suna cin karensu babu babbaka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel