Kotu ta datse igiyar auren shekara 10 bayan mata ta zargi miji da halin bera

Kotu ta datse igiyar auren shekara 10 bayan mata ta zargi miji da halin bera

- Matar aure ta zargi mijinta da sace mata 'yan kudadenta da take boyewa a ma'adanarta

- Bayan zargin sata, matar mai suna Shakirat ta yi zargin cewa mijinta ya na yi mata barazanar cewa zai watsa mata ruwan asid

- Alƙali Ademola Odunade, shugaban kotun al'adu ta Mapo da ke Ibadan, ya warware igiyar auren don wanzuwar zaman lafiya

Kotun al'adu da ke yankin Mapo a Ibadan ta datse igiyar auren da ya shafe shekaru goma tsakanin wani ɗan achaɓa, Akinola Olaogun, da matarsa, Shakirat, sakamakon zargin halin bera da barazanar watsa mata ruwan asid da ya ke yi.

Da yake yanke hukunci, alƙali Ademola Odunade, shugaban kotun ya warware igiyar auren don wanzuwar zaman lafiya a tsakaninsu.

Odunade ya raba ƴaƴan su guda biyar inda ya miƙawa Olaogun ƴaƴansu guda biyu na farko yayin da Shakirat ta karɓi guda ukun ƙarshe.

DUBA WANNAN: Ke mayya ce idan mijinki ya tsiyace bayan kun yi aure - Malamar Mata

Kazalika, ya kuma gindayawawa Olaogun sharadin biyan dubu sha biyar ₦15,000 duk wata a matsayin kuɗin ciyar da yaran.

Kotu ta datse igiyar auren shekara 10 bayan mata ta zargi miji da halin bera
Kotu ta datse igiyar auren shekara 10 bayan mata ta zargi miji da halin bera @Punch
Asali: Twitter

Da farko, an zargi Olaogun da yi wa matarsa barazana da cewa zai watsa mata ruwan acid saboda ta gudu, ta barshi, zuwa wurin masoyinta da suke rayuwa tare.

Daga bisani, Olaogun ya amsa, a gaban kotun, cewa yana dukan matarsa.

DUBA WANNAN: Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi martanishagube a kan tsine mata a Masallatai

"Mai Shari'a, gaskiya ne nayi barazanar watsa ruwan acid ga matata da kuma babarta, amma barazana ce kawai don su ji tsoro ba wai hakan nake nufi da gaske ba,'' a cewarsa.

Shakirat ta roƙi kotun ta amsa addu'arta ta neman a raba aurensu, don ganin ra rabu da ƙaya.

"Yana dukana kuma yana yi min barazanar wanka da ruwan asid. Yana satar kuɗi daga ma'ajiyata.

"Daɗin daɗawa shi manemin mata ne, kuma bai san ciwon kansa ba", kamar yadda Shakirat ta faɗawa kotu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng