Ke mayya ce idan mijinki ya tsiyace bayan kun yi aure - Malamar Mata

Ke mayya ce idan mijinki ya tsiyace bayan kun yi aure - Malamar Mata

- Malamar mata, marubuciya, kuma fasto a Cocin Agape Ministries, Funke Adejomo, ta ce mayun mata sune silar talaucewar maza da yawa

- A cewar Funke, zubar da mutunci ne mace ta ke rokon mijinta kudin sayen rigar mama

- Funke ta zaburar da mata su tashi domin neman na kansu, su tsaya da kafafunsu, su daina dorawa mazajensu dukkan nauyin rayuwarsu

Funke Adejomo, marubuciyar Najeriya kuma fasto a cocin Agape Ministries, ta bayyana cfewa duk macen da arziƙin mijinta ya karye bayan ya aureta, bata da maraba da mayya.

Ta faɗi hakan lokacin da take magana akan irin muhimmiyar rawa da yakamata mata su taka a gidan mazajen su yayin wa'azi a coci.

Lokacin da take yin huɗuba,Funke,ta caccaki mata masu bajewa a gidan miji suyi ta haifu ƴa'ƴa kuma su bar mazajensu da wahala.

DUBA WANNAN: Na yi aiki da Gowon, Buhari, da OBJ amma yanzu sai na roki abinci - Kaftin Mai ritaya

"Bai kamata ki zamo mara amfani ba,ace sai kin roƙi mijinki ya baki kuɗi kafin ki sai rigar mama.Wannan abubuwa ne da ke zubar da daraja da kuma kimar ƴa mace,'' A cewar Funke.

Ke mayya ce idan mijinki ya tsiyace bayan kun yi aure - Malamar Mata
Funke Adejumo @Funke
Asali: Instagram

Sannan ta cigaba da cewa; "kada ku ɗorawa mazajenku nauyin ƴayanku don ba nasu bane su kaɗai ya kamata kuma ku bada gudunmawa duk ƙanƙantar ta.

DUBA WANNAN: Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi shagube a kan tsine mata a Masallatai

"Kiyi abin kirki da rayuwarki a matsayinki na mace. An halicce ki ne don ki ƙarawa abubuwa armashi.

"Na ƙarawa aurena armashi. Mijina da kansa ya kalli cikin idanuna yace ina son na aureki'.Kada ki zama mace mai roƙo.''

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, za a fafata da 'yan Najeriya 9 a zaben da za a gudanar ranar uku ga watan Nuwamba a kasar Amurka

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa baya ga zaɓen shugaban ƙasa da za'a gudana a ƙasar Amurka, akwai zaɓen gwamnoni a jihohi goma sha ɗaya da manyan birane gida biyu, da ƙarin wasu jihohin da kuma ƙananan hukumomi.

Zaɓen ƴan majalisu 435 da sanatoci 100 shima yana cikin jadawalin zaɓen da za'a fafata a cikinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel