EndSARS: Ba za mu tilasta wa kowani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba –Hukumar yan sanda

EndSARS: Ba za mu tilasta wa kowani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba –Hukumar yan sanda

- Hukumar yan sanda ta yi martani a kan rahoton cewa tana shirin sallamar jami'anta da suka ki komawa bakin aiki bayan zanga-zangar EndSARS

- PSC ta bayyana hakan a matsayin karya inda tace ba za ta tilasta wa jami'anta dawowa aiki ba

- Sai dai ta ce abu guda da za ta iya yi shine ta lallashe su domin suna cikin juyayin rashi da suka yi a yanzu

Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ba za ta tursasa ma kowani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Hukumar PSC din ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, a cikin wata sanarwa daga Shugaban harkokin labaranta da hulda da jama’a, Ikechukwu Ani.

Jawabin martani ne ga wata wallafar jarida wacca ta bayyana cewa hukumar ta yi barazanar korar duk jami’an da suka ki dawowa bakin aiki.

Hukumar ta ce rahoton kanzon kurege ne, cewa zai zama rashin hankali tsantsa ga hukumar idan ta kori kowani dan sandan da ya ki komawa aiki.

EndSARS: Ba za mu tilasta wa kowani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba –Hukumar yan sanda
EndSARS: Ba za mu tilasta wa kowani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba –Hukumar yan sanda Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Tsohon dan takarar shugaban kasa, Olapade Agoro, ya rasu

A baya dai mun ji yadda zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar ya koma rikici bayan sojoji sun harbi masu zanga-zangar lumana a Lekki toll gate da ke jihar Lagas.

Tuni dai yan sanda da dama suka yi watsi da ayyukansu bayan barkewar rikicin.

A cikin jawabin Mista Ani, ya ce abunda kawai hukumar za ta iya yi shine ta roki jami’an yan sanda su koma bakin aiki duba ga yawan rayukan da yan sandan suka rasa a yayin zanga-zangar.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin 2023: Ba za mu iya cewa ga yankin da magajin Buhari zai fito ba, Buni

Ya kuma bayyana cewa hukumar na cikin halin juyayi don haka rahoton barazanar korar zai zama rashin hankali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng