Tsohon dan takarar shugaban kasa, Olapade Agoro, ya rasu
- Allah ya yiwa tsohon dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar National Action Council (NAC), Cif Olapade Agoro rasuwa
- Agoro ya rasu yana da shekaru 77 bayan ya yi fama da yar rashin lafiya
- Daya daga cikin 'ya'yansa ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa
Tsohon dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar National Action Council (NAC), Cif Olapade Agoro ya mutu yana da shekaru 77 a duniya.
A cewar majiyoyi cikin iyalansa, Agro ya rasu a safiyar ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, bayan yar gajeriyar rashin lafiya, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Da yake tabbatar da batun mutuwar nasa, dan marigayin, Adebo Agoro, ya ce : “mahaifina ya mutu bayan wata yar gajeriyar rashin lafiya.”
KU KARANTA KUMA: Shugabancin 2023: Ba za mu iya cewa ga yankin da magajin Buhari zai fito ba, Buni
An haifi Dr. Agoro a ranar 9 ga watan Oktoba, 1943 a kauyen Ajibabi da ke Ibadan. Ya fito a tsatson yariman masarautar Atapami da ke Itapa Ijjesha.
Iyayensa sune marigayi Omo-Oba Owa ‘Tapa Joshua Alaba Agoro da matarsa marigayiya Dorcas Oyejola Asabi Agoro.
A wani labarin kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga Shugaban kungiyar wasanni ta Olympics a Najeriya, Injiniya Habu Ahmed Gumel, a kan mutuwar matarsa, Hajiya Ladi Gumel.
Buhari a cikin wani jawabi daga mai ba shi shawara a kafofin watsa labar, Mallam Garba Shehu, a yau Laraba, ya kuma mika sakon jaje ga iyalai da makusantan marigayiyar.
Ya kuma yi kira garesu a kan su dauki dangana tare da koyi da kyawawan dabi’un marigayiyar sannan su yi alfahari da shaidar rayuwa ta gari da ta samu wajen kyautata kusancinta da Mahallicinta, jaridar Aminiya ta ruwaito.
Shugaban kasar ya yi addu’ar neman Allah ya jikanta da Rahama tare da bai wa iyalanta juriya ta rashin da suka yi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng