Bayan Kuskure a Wasan Arsenal, Malamin Addini Ya Faɗi Mai Lashe Gasar UCL

Bayan Kuskure a Wasan Arsenal, Malamin Addini Ya Faɗi Mai Lashe Gasar UCL

  • Wani fasto daga birnin Umuahia a jihar Abia, Joel Atuma, ya yi hasashen wasan karshe tsakanin PSG da Inter Milan a gasar zakarun Turai ta 2025
  • Atuma ya bayyana hakan a cikin bidiyo inda ya ce PSG za ta lashe kofin saboda wani abu da ya shafi Fafaroma
  • Yayin ya biyo bayan tafka kuskure a hasashen da Faston ya yi a wasan Arsenal da PSG da aka buga a ranar Laraba da ta gabata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Umiahia, Abia - Wani fasto, Joel Atuma, ya bayyana hasashensa dangane da wasan karshe na gasar zakarun Turai na shekarar 2025 da ke tafe.

A baya, Faston ya yi hasahen wasan Arsenal a gasar zakarun Turai inda mutane suka yi ta martanin bayan malamin ya yi kuskure a hasashen na shi.

Fasto ya magantu kan gasar zakarun Turai
Fasto ya fadi kungiyar da za ta lashe gasar zakarun Turai. Hoto: @PSG_inside, @DougieCritchley.
Asali: Twitter

Fasto ya magantu kan wasan Inter da PSG

A cikin bidiyon YouTube da Legit.ng ta kalla, Atuma ya yi hasashen kungiyar da za ta "lashe kofin gasar zakarun Turai" a wannan shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a buga wasan karshe na UCL na shekarar 2025 a Allianz Arena da ke birnin Munich, Jamus, a ranar 31 ga Mayun 2025.

Kungiyar PSG ta Faransa ce za ta kara da Inter Milan daga Italiya, kamar yadda aka tabbatar da jadawalin wasan karshe.

A cewar Atuma, wanda ke da coci a Umuahia, PSG za ta doke Inter Milan domin lashe gasar zakarun Turai ta 2025.

A cikin bidiyon da ya wallafa, faston ya ce PSG za ta yi nasara ne "saboda Fafaroma" inda ya ce zai yi bayani daga baya.

Wasan karshe na gasar zakarun Turai na 2025 ya hada Inter Milan, zakarun Italiya, da PSG, babbar kungiya daga kasar Faransa.

Atuma ya ce:

"Lokacin PSG ne na daukar kofin. Ko da ba tare da Kylian Mbappé ba, hakan zai faru."
"Ku saurara, PSG za ta zama zakaran Turai a karshen watan Mayu. Saboda Paparoma ne."
"Zan dawo in fayyace abin da ya faru, duk lokacin da Fafaroma ya rasu."

Inter ta doke Barcelona 7-6 yayin da PSG ta lallasa Arsenal 3-1 bayan zagaye biyu.

A gefe guda, Inter ba za ta yi ganganci ba da lafiyar Lautaro Martinez ba kafin wasan karshe da PSG.

Rahotannin sun tabbatar da cewa Martinez ba zai buga wasa da Torino a gasar cikin gida ta Serie A ba.

Legit Hausa ta yi magana da matashi

Magoyin bayan kungiyar Barcelona, Adam ya ce Fasto ya saka musu rai a makon jiya.

Matashin da aka fi sani da mai Barca ya ce duk da Fasto ya ce Arsenal za su yi nasara amma bai ji daɗin cire su ba.

"Duk da hasashen bai min dadi ba amma na so na ga Barca a final, to ga shi ma har da Arsenal din an cire mu."

- Cewar Adam

Ya ce dalilin wancan hasashen ba zai sakankance ba duk da yafi son PSG ta kashe kofin.

Zakarun Turai: Fasto ya yi hasashen wasan Arsenal

A baya, kun ji cewa Malamin coci, Joel Atuma ya yi hasashen wasan Arsenal inda ya ce za ta doke PSG a wasan kusa da karshe sannan ta fafata da Barcelona a gasar karshe ta UCL na 2025.

Faston ya ce za a sake ganin karo tsakanin Arsenal da Barcelona kamar yadda ya faru a 2006, sai dai Arsenal za ta yi nasara yanzu.

Sai dai malamin ya tafka kuskure domin kuwa Arsenal ta sha kashi a hannun PSG a wasan da suka buga karo na biyu a birnin Paris a ranar Laraba da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.