Ahmed Musa Ya Ba Super Eagles Sirrin Doke Kasar Angola a Gasar AFCON 2023

Ahmed Musa Ya Ba Super Eagles Sirrin Doke Kasar Angola a Gasar AFCON 2023

  • Ahmed Musa ya na cikin kwararrun ‘yan wasan wadanda aka dade ana yi da su a nahiyar Afrika
  • ‘Dan wasan gaban na Sivasspor ya fadawa ‘yan kwallon Super Eagles yadda suka lashe AFCON 2013
  • Shekaru 10 da suka wuce, Najeriya ta dauko kofin gasar nahiyar Afrika daga kasar Afrika ta Kudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Cote d’ Ivoire - Tsohon ‘dan wasan Arsenal, Alex Iwobi ya yi bayanin yadda Najeriya ta ke shiryawa Angola a gasar AFCON 2023.

‘Dan wasan na kungiyar Fulhman yana cikin tawagar Super Eagles da ke Cote d’ Ivoire, ya zanta da ‘yan jarida a ranar Alhamis.

AFCON 2023
Super Eagles a AFCON 2023 Hoto:@NGSuperEagles @Thenff
Asali: Twitter

Super Eagles tana harin AFCON 2023

Soccernet ta rahoto Alex Iwobi yana cewa da gaske su ke yi wajen ganin sun lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika wannan karo.

Kara karanta wannan

AFCON: Tauraron S/Eagles, Osimhen ya samu matsala za a buga wasan Afrika ta Kudu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan Jose Paseiro ya yi nasara, zai zama karon farko da Super Eagles ta yi galaba a gasar tun bayan lokacin Stephen Keshi a 2013.

Iwobi ya ce ‘yan kwallon S/Eagles su na da kishin ruwan kofin, za suyi bakin kokarinsu wajen ganin sun yi waje da Angola.

Kokarin Najeriya a gasar AFCON

Kafin yanzu Najeriya ta gwabje makwabciyarta kasar Kamaru da ci 2-0 ta hannun Ademola Lukman, Tori ta fitar da labarin nan.

Najeriya tana cikin kasashen da su ke tabuka abin kirki a gasar 2023, kwallo guda kurum aka zurawa Stanley Nwabali har yanzu.

Iwobi mai shekara 27 ya ce tsohon ‘dan wasan na Kano Pillars da Leicester ya fada masu su rabu da surutun masu yin surutai.

Iwobi a kan gudumuwar Ahmed Musa a AFCON

"Musa ya fada mana yadda suka lashe AFCON 2021. Yana samar da irin wannan yanayi kuma kowa yana da kishi."

Kara karanta wannan

Zanga zanga ya barke a Kaduna saboda kashe wanda ya hana sace kuri’un zabe

"Ya (Ahmed Musa) yana so ya zaburar da mu, mu samu irin wannan nasara."
"Musa ya fada mana mu yi watsi da surutan da ake yi a waje. Mu na so mu sake yin haka."
"Za mu fara da zagayen kwata-fainal, sai mu bada duka karfinmu 100 bisa 100."

- Alex Iwobi

Ahmed Musa a bencin AFCON 2023

Ahmed Musa mai 'da daya bai buga wasa a gasar da ake bugawa a yanzu ba. Masoya suna ta kira ga koci ya rika amfani da shi.

‘Dan wasan gaban yana cikin kwararrun da Super Eagles ta dogara da shi, yana cikin tawagar da ta dauki kofi a AFCON 2013.

Asali: Legit.ng

Online view pixel