Zanga Zanga Ya Barke a Kaduna Saboda Kashe Wanda Ya Hana a Sace Kuri’un Zabe

Zanga Zanga Ya Barke a Kaduna Saboda Kashe Wanda Ya Hana a Sace Kuri’un Zabe

  • Wani mutumi mai shekara 40 ya mutu a wajen zabukan cike gurbi da INEC ta shirya a karshen makon jiya
  • ‘Yan daban siyasa sun kashe Mansir Shafiu a yunkurin fashin kuri’u a zaben da PDP ta lashe a yankin Igabi
  • Mutane sun yi zanga-zanga domin nuna fushinsu, sun nemi su aukawa gidan Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Wani bawan Allah mai suna Mansir Shafiu ya hallaka a wajen zaben cike gurbi da aka shirya a garin Kaduna.

An kashe Mansir Shafiu ne lokacin da ya yi kokarin hana ayi magudin zabe, Daily Trust ta kawo labarin nan a ranar Lahadi.

Zabe a Kaduna
Zabe a Kaduna (Hoton nan bai da alaka da labarin) Hoto; Getty Images
Asali: Getty Images

Kaduna: An kashe mutum wajen zabe

Kara karanta wannan

Bai kamata a fara sukar gwamnatin Tinubu ba daga yanzu, Shehu Sani ya bayyana dalili

Marigayin ya nemi taka burki da aka yi yunkurin sace akwati a yankin Rigachikun da ke karamar hukumar Igabi a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani wanda ya shaida abin da ya faru ya ce wani daga cikin ‘yan iskan da suka zo fashin kuri’un ne ya daba masa wuka.

...An birne wanda ya rasu a Kaduna

Da aka zanta da wani ‘dan jam’iyyar PDP kuma daya daga cikin yaran Hussaini M. Jalo a yankin Igabi, ya tabbatar da zancen.

‘Dan siyasar ya ce an birne mamacin tun safiyar Lahadi kamar yadda musulunci ya tanada.

Hussaini Muhammad Jalo wanda ya lashe zaben ya sadaukar da nasararsa ga Allah SWT da kuma matashin da aka kashe.

'Dan majalisan Kaduna ya yi magana

‘Dan majalisar ya sha alwashin cewa dole ne a gudanar da bincike domin gano wadanda suka yi wannan mummunan aiki.

Kara karanta wannan

Aikin gama ya gama: Dan takarar PDP ya sha kaye a zaben cike gurbi a Yobe, an fadi wanda ya lashe

Jam’iyyar PDP ta na zargin an nemi a tada rikici wajen zaben a Unguwar Yelwa Birinin Yero, Kwarau, Mando da kuma Joga.

Zanga-zanga a jihar Kaduna

Kamar yadda Vanguard ta rahoto, mutuwar wannan mutum wajen zaben cika gurbin da aka shirya ya jawo zanga-zanga.

Rahotanni sun ce an yi zanga-zanga a garin Rigachikun a ranar Lahadi, a karshe jami’an tsaro su ka fatattaki mutanen.

Sojoji sun hana a kona gidan Yusuf Zailani wanda ake zargin yana da hannu a kisan kan duk da babu hujja game da hakan.

Yusuf Zailani da siyasar Kaduna

Kafin ya bar kujerar shugaban majalisar dokokin Kaduna, ana da labari Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani ya saki wasu bayanai.

‘Dan majalisar na Igabi ta yamma ya ce an yi yunkurin soke kotun shari’a da na gargajiya karkashin jagorancin Nasir El-Rufai

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel