Matar Ahmed Musa ta haifi ɗa namiji
Matar babban ɗan wasar tawagar Super Eagles na Najeriya, Ahmed Musa ta haihu kamar yadda fitaccen ɗan wasar ya sanar a dandalin sada zumunta.
Julie ta haifi ɗa namiji, wannan shine haihuwar ta na biyu tare da ɗan kwallon. A baya ta haifa masa ƴa mace.
Ahmed Musa yana da wasu ƴaƴa biyu da tsohuwar matarsa ta haifa masa kafin ya auri Julie.
DUBA WANNAN: Hotuna: Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya tafi Senegal don hallartar jana'izar ɗan Sheikh Inyass
Da ya ke sanar da labarin, ɗan kwallon ya mika godiyar sa ga Allah da kuma dukkan wadanda suka taimaka masa da iyalinsa da addu'a.
Ya rubuta;
"Rai kyauta ce daga Allah kuma Allah cikin ikonsa ya bamu kyautar da kuɗi ba za ta iya siya ba. Allah ya bawa iyali na ɗa namiji a safiyar yau... Mahaifiyar ɗan da ɗan duk suna cikin ƙoshin lafiya. Mun gode da addu'a ga goyon baya."
A wani labarin, Dagajin ƙauyen Oose Agbedu Ajibawo a Owode-Yewa, a ƙaramar hukumar Yewa ta Kudu na jihar Ogun ya suma an garzaya da shi asibiti bayan an gabatar masa da hujjar cewa yana yi wa yarsa fyaɗe.
Dagajin ƙauyen da ƴan sanda suka kama saboda zargin yi wa yarsa mai shekaru 15 fyade, ya musanta zargin da ake masa.
Amma yayinda ɗaya daga cikin tsohuwar matarsa ta gaskata zargin da ƴarsa ta yi, ya yanke jiki ya faɗi sumamme kuma aka garzaya da shi asibiti inda ya farfaɗo a can.
Kakakin ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan ciki wata sanarwa da ya fitar kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Ya yi bayanin cewa yarinyar ta yi ƙorafin cewa mahaifinta ya kwashe shekaru hudu yana lalata da ita tun tana ƴar shekaru 11.
Kakakin ƴan sandan ya ce abin ya faru da ita ta koka cewa tana samun matsala da mafitsarar ta sakamakon abinda mahaifinta ya aikata.
Ya ce, "wacce abin ya faru da ita ta shaida wa ƴan sanda cewa mahaifiyarta ta rasu lokacin tana da shekaru biyu kuma mahaifinta bai bari ta san ƴan uwan mahaifiyarta ba.
"Hakan yasa ba ta da zaɓi sai cigaba da zama tare da shi duk da cewa ya kan ci zarafin ta lokaci zuwa lokaci."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng