Ahmed Musa Ya Samu Gagarumar Cigaba, Ya Samu Shiga Kungiyar Kwallon Kafan Turkiyya ta Sivasspor

Ahmed Musa Ya Samu Gagarumar Cigaba, Ya Samu Shiga Kungiyar Kwallon Kafan Turkiyya ta Sivasspor

  • Ahmed Musa ya bar kungiyar kwallon kafan Turkiyya mai suna Fatih Karagumruk inda ya saka hannu kan yarjejejniyarsa da Sivasspor
  • Har yanzu ba a fitar da bayanan kwangilar ba a fili amma an tattaro cewa yasa hannu kan yarjejeniyar ta tsawon shekaru biyu
  • Kocin kungiyar ne da kansa ya nemi fitaccen 'dan kwallon kafar inda ya nemi su yi yarjejeniyar da matashin mai shekaru 29

Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, hya bar kungiyar kwallon kafan Turkiyya Fatih Karagumruk inda ya samu shiga wata gagagrumar kungiyar mai suna Sivasspor a yarjejeniyar shekaru biyu.

Zakaran 'dan wasan kwallon kafan wanda ya kwashe shekara daya a Karagumruk ya yanke hukuncin barin kungiyar ne domin ya gangara Sivasspor.

Musa Ahmed
Ahmed Musa Ya Samu Gagarumar Cigaba, Ya Samu Shiga Kungiyar Kwallon Kafan Turkiyya ta Sivasspor. Hoto daga Kevin C. Cox
Asali: Getty Images

An tattaro cewa, Kocin Riza Calimbay ne ya bukaci karbar matashin 'dan kwallon mai shekaru 29 a duniya kuma sun gana a ranar Alhamis da ta gabata.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Bindiga Ta Ki Tashi Yayinda Wani Yayi Kokarin Kashe Mataimakiyar Shugaban Kasar Argentina

Fanatic sun rahoto cewa, kungiyar ta shiga yarjejeniya da kwararre kuma gogaggen 'dan wasan ne domin inganta kungiyar kafin zuwan kakar wasannin UEFA Europa Leagues.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Musa yayi wa kungiyoyin wasan kwallon kafa aiki kamar su Kano Pillars, VVV-Venlo, CSKA Moscowa, Leicester City, Al Nasssr da Fatih Karagumruk.

A yayin da Sports Brief ta tuntubi fitaccen 'dan wasan kwallon domin tabbatar da sabuwar yarjejeniyar, yayi martani da:

"Tabbas."

Musa ya bar Fatih Karagumruk da amincewar kowanne bangare

Kamar yadda kungiyar kwallon kafan ta tabbatar, an dakile kwantiragin Ahmed Musa ne bayan yarjejeniya tsakanin kungiyar wasan kwallon kafan da fitaccen 'dan wasan.

Takardar tace:

"Mun sahhalewa juna bayan amincewa tsakaninmu da kwararren 'dan wasan kwallon kafa Ahmed Musa, wanda ya shiga kungiyar mu a 2021 zuwa 2022."

Kara karanta wannan

Mu Kake Kira Yara, Zamu Koya Maka Hankali: Wike Ya Yiwa Ayu Raddi

'Yan Fashi Sun Shiga Gidan Aubameyang, Sun Lallasa Shi tare da Masa Sata

A wani labari na daban, zakaran kwallon kafa na kungiyar Barcelona, Pierre-Emerick Aubameyang, ya shiga tashin hankali bayan 'yan fashi da makami sun kutsa gidansa a sa'o'in farko na ranar Litinin, cewar kungiyar kwallon kafan ta Spain.

"A halin yanzu yana lafiya amma a tsorace," wata majiya daga Barcelona ta sanar da AFP yayin tabbatar da rahoton manema labarai.

A kalla 'yan fashin hudu ne suka kutsa gidansa dake Castelldefels kusa da Barcelona ta lambunsa inda suka yi barazana garesa da matarsa da bindigogi da sandunan karfe, Daily El Pais suka rahoto.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel