Bidiyo: Bindiga Ta Ki Tashi Yayinda Wani Yayi Kokarin Kashe Mataimakiyar Shugaban Kasar Argentina

Bidiyo: Bindiga Ta Ki Tashi Yayinda Wani Yayi Kokarin Kashe Mataimakiyar Shugaban Kasar Argentina

  • Wani ya yi kokarin kashe mataimakiyar shugabar kasan Argentina a bainar jama'a amma aka samu matsala
  • A bidiyo, mutumin ya harba bindigar amma taki tashi, wannan abu ya baiwa mutane mamaki
  • Ministar Tsaron Kasar ya bayyana cewa an damke mutumin kuma ana gudanar da bincike

Argentina - Mataimakiyar Shugaban kasar Argentina, Cristina Kirchner, ta tsallaka rijiya da baya ranar Alhamis yayinda wani yayi kokarin kasheta cikin jama'a.

A cewar AFP, wanda ake zargi wani dan kasar Brazil ne yayi kokarin kasheta kusa da gidanta dake Buenos Aires amma bindigar taki tashi.

Shugaban kasar Argentina, Alberto Fernandez, ya yi jawabi ga al'ummar kasar bisa wannan abinda ya faru.

Yace:

"Cristina na nan da rai, amma cikin ikon Allah bindigan mai dauke da harsasai biyar yaki tashi duk da cewa an harba."

Kara karanta wannan

Tsohon Minista Ya Bayyana Halin da Lafiya 'Dan Takarar APC, Bola Tinubu, Take Ciki

"Wannan shine abu mafi muni da ya faru tun bayan rusa demokradiyya a 1983."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyo ya nuna lokacin da mutumin ya kai bindigar har wajen gaban goshin mataimakiyar shugaban kasar kuma ya harba.

Kalli bidiyon:

Ministan Tsaron kasar, Anibal Fernandez, ya bayyana cewa an damke mutumin kuma ana gudanar da bincike kan lamarin.

Bayan ga haka, shugaban kasa Fernandez ya bada hutu ranar Juma'a don mutane suyi nazari kan lamarin tare da taya mataimakiyar shugabar kasar murnar tsallake rijiya da baya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel