Ina zan gan shi?: Ahmed Musa ya shirya taimakon tsohon zakaran Olympic dake cike kwararon titi a Legas

Ina zan gan shi?: Ahmed Musa ya shirya taimakon tsohon zakaran Olympic dake cike kwararon titi a Legas

  • Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, yana kokarin ganin ya gana da tsohon zakaran wasannin Olympic Bassey Etim
  • An gano Bassey Etim a yankin Ajah na jihar Legas, inda mai shekaru 56 a duniya yake taimakon jama'a wurin cike kwazazzaban titi
  • Wani bidiyon Bassey ya yadu wanda ke nuna zakaran Olympic din a tituna amma kyaftin Ahmed Musa tuni ya nuna yana son taimakonsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kyaftin din kungiyar wasan kwallon kafa ta Najeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa, yana son taimakawa tsohon zakaran wasannin Olympic, Bassey Etim, wanda aka gani a yankin Ajah ta jihar Legas yana cike kwazazzaban kan titi.

A baya ana kiran zakaran da 'Iron bar', an gan shi a wani sashin titin Ado/Badore a jihar Legas.

Ahmed Musa
Ina zan gan shi?: Ahmed Musa ya shirya taimakon tsohon zakaran Olympic dake cike kwararon titi a Legas
Asali: Instagram

Mawakin Najeriya, Oc Cares, ya bayyana yadda ya ga Bassey na aikin taimakon al'umma a tituna na tsawon lokaci, lamarin da yasa ya neme shi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

Bassey Etim, wanda ya taba cin kambun zinari na wasannin Commonwealth a Malta a 1983, ya bayyana cewa ya samu rauni yayin wakiltar Najeriya a wasannin Olympic na 1984.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Etim mai shekaru 56 ya karar da duk kudaden da ya samu wurin jinya, inda yayi ikirarin cewa Najeriya tayi watsi da shi.

Haifaffen jihar Cross River din ya ce:

"Na samu rauni kuma ko da na dawo, Najeriya ta ki daukar nauyin jinyata. Saboda haka ne nayi amfani da dukkan kudaden na koma Amurka a watan Satumban 1985 domin jinyar kaina.
"Amma duk da haka nakan fito aikin sa kai ga kasa. Mutane na cewa a kan mene zan yi haka? Ba su kula da ni ba ai.

Bidiyon da ya yadu ne ya janyo hankalin Ahmed Musa wanda ya bukaci yadda zai yi ya same shi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, a Mimbarin Coci yana ihun 'Ku Yabi Ubangiji' ya janyo cece-kuce

Kamaru: Ahmed Musa ya gwangwaje Masallacin Garoua da tallafin $1500

A wani labari na daban, Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa, ya gwangwaje wani masallacin Juma'a da ke Garoua a kasar Kamaru da tallafin $1,500 bayan idar da sallar Juma'a, Punch Sports Extra ta ruwaito.

Masallacin wanda ya ke kusa da sansanin 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya a Garoua, shi ne inda 'yan wasan ke sallah a kowacce rana tun bayan isar su yankin arewacin kasar Kamaru a ranar 5 ga watan Janairu.

Punch ta ruwaito cewa, ana sa ran wannan tallafin zai taimaka wa malaman masallacin wurin kammala ginin, wanda har yanzu ake kan yi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel