Kamaru: Ahmed Musa ya gwangwaje Masallacin Garoua da tallafin $1500

Kamaru: Ahmed Musa ya gwangwaje Masallacin Garoua da tallafin $1500

  • Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa, ya bai wa wani Masallacin Juma'a tallafi a garin Garoua da ke Kamaru
  • Tun bayan saukar 'yan wasan kwallon kafa na Super Eagles a Kamaru, wannan masallacin su ke yin sallah 5 a kowacce rana
  • Ana sa ran tallafin $1500 da ya bai wa masallacin zai taimaka wurin kammala ginin da ake yi a halin yanzu

Kamaru - Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa, ya gwangwaje wani masallacin Juma'a da ke Garoua a kasar Kamaru da tallafin $1,500 bayan idar da sallar Juma'a, Punch Sports Extra ta ruwaito.

Masallacin wanda ya ke kusa da sansanin 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya a Garoua, shi ne inda 'yan wasan ke sallah a kowacce rana tun bayan isar su yankin arewacin kasar Kamaru a ranar 5 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

AFCON: Matasa sun dira gidan dan kwallon da ya zubar da fenariti a wasar Sierra Leone da Guinea

Ghana: Ahmed Musa ya gwangwaje Masallacin Garoua da tallafin $1500
Ghana: Ahmed Musa ya gwangwaje Masallacin Garoua da tallafin $1500. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Punch ta ruwaito cewa, ana sa ran wannan tallafin zai taimaka wa malaman masallacin wurin kammala ginin, wanda har yanzu ake kan yi.

Kamar yadda wani daga cikin 'yan kungiyar ya ce, Musa, wanda ya bayyana sau daya wurin maye gurbi a gasar, ya sanya a ran sa cewa zai bayar da tallafi wurin ginin masallacin tun bayan da ya fara sallah a ciki.

"Wannan hanyar shi ce ta nuna godiyar sa gare su," dan kungiyar, wanda ya bukaci a boye sunan sa ya ce.

Musa zai yi bayyana ta biyu a gasar kwallon kafan inda Najeriya za ta buga da kasar Tunisia a zagaye na 16 a filin wasan Roumde Adjia da ke Garoua a ranar Lahadi.

Ahmed Musa yayi martani mai zafi bayan sun sha da kyar a filin wasa a Kaduna

Kara karanta wannan

Borno: Ɗalibin sakandare ya keta makogwaron ɗalibin ƙaramin aji da reza don ya sa shi aiki ya ƙi yi

A wani labari na daban, fitaccen dan wasan kwallon kafa Ahmed Musa ya nuna damuwarsa da rashin jin dadinsa a kan mummunan lamarin da ya faru a filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna a ranakun karshen mako.

Kano Pillars sun karba bakuncin Akwa United a wani wasa da manyan kungiyoyin kwallon kafan suka yi.

Amma kuma magoya bayan Kano Pillars sun kutsa filin wasa a fusace domin lakadawa alkalan wasa duka bayan sun soke kwallon da ta shiga raga a minti na 85 na wasan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel