Bidiyon Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, a Mimbarin Coci yana ihun 'Ku Yabi Ubangiji' ya janyo cece-kuce

Bidiyon Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, a Mimbarin Coci yana ihun 'Ku Yabi Ubangiji' ya janyo cece-kuce

  • Bidiyon Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam'iyyar APC na kasa, a kan mumbarin coci yayin da ake bauta ya janyo cece-kuce
  • A wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani, an ga sanatan yana ihun 'ku yabi Ubangiji' a cikin Kiristoci a wata coci
  • Kamar yadda bidiyon ya nuna, sanatan yana sanye da bakar hula tare da babbar riga wacce launinta ruwan kasa ne mai duhu kuma rike da amsa kuwwa

'Yan Najeriya a kafafen sada zumuntar zamani a halin yanzu suna ta martani kan wani bidiyo dake yawo na shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu, inda ya halarci wata jana'iza a coci.

A daya daga cikin lokutan bauta na Evangelical Church of West Africa EKWA an ga shugaban jam'iyyar mai mulki na kasa a kan mumbarin cocin.

Kara karanta wannan

Jarumar Mata: Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Adamu Abdullahi
Bidiyon Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, a Mimbarin Coci yana ihun 'Ku Yabi Ubangiji' ya janyo cece-kuce. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bidiyon, an ga Sanata Adamu sanye da hula kuma yana kan mumbari inda yake gaida jama'ar dake bauta.

"Ku yabi Ubangiji," yace yayin da yake daga murya ga masu bautar rike da amsa kuwwa kuma yana tsaye.

Har dai a yayin rubuta wannan rahoton, Legit.ng bata san inda aka nadi bidiyon ba.

Bidiyo: Matasa sun je har gidan Sheikh Yabo don jinjina masa kan yadda yake cashe gwamnati

A wani labari na daban, fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Bello Yabo na jihar Sokoto, ya samu gaisuwar ban girma da jinjina daga wasu matasa har gidansa.

Matasan da suka yi tururuwar zuwa gidan Shehin Malamin, sun bayyana cewa yadda yake fadawa gwamnati gaskiya ne yasa suka ce dole su je su yaba masa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

A bidiyon da aka nada na lokacin da matasan suka je gidan malamin, an gan shi tsaye yayin da matasan suka zagaye shi sun yaba masa yadda ya saka fadin gaskiya a gaba ga gwamnati a kan wannan rashin tsaro da yayi kamari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel