Jigo a garinsu Buhari ya soki yan Najeriya kan daura alhakin faduwar Super Eagles da magana da shugaban kasar

Jigo a garinsu Buhari ya soki yan Najeriya kan daura alhakin faduwar Super Eagles da magana da shugaban kasar

  • Shugaban kungiyar kwallon kafa ta jihar Katsina ya soki ‘yan Najeriya da suka daura alhakin faduwar Super Eagles a gasar cin kofin Afrika kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Alhaji Aminu Balele Kurfi ya ce kawai dai suna kai hare-haren wuce gona da iri ne domin babu alaka tsakanin faduwar yan wasan da wayar da suka yi da Buhari
  • Ya yi kira ga jama’ar kasar da su yi wa yan wasan na Super Eagles addu’an samun nasara a wasanninsu na gaba maimakon ganin laifin wani

Katsina - Shugaban kungiyar kwallon kafa ta jihar Katsina, Alhaji Aminu Balele Kurfi, ya nuna takaici da rashin jin dadi kan yan Najeriya da ke ci gaba da dora wa shugaban kasa Muhammadu Buhari laifin rashin nasarar Super Eagles a gasar cin kofin Afrika da ke gudana.

Kara karanta wannan

Buhari: Ka da 'Yan Najeriya su cire tsammani daga Super Eagles

Idan za a tuna, Shugaba Buhari ya yi magana da yan wasan Super Eagles kafin karawarsu da yan wasan kasar Tunusiya a ranar Lahadi, 23 ga watan Janairu.

A ganawar tasu ya jinjinawa yan wasan da jami'an kungiyar inda ya bukace su da su tabbatar da yin nasara a wasansu da kasar Tunisiyan.

Jigo a garinsu Buhari ya caccaki 'yan Najeriya kan daura alhakin faduwar Super Eagles da magana da Buhari
Jigo a garinsu Buhari ya caccaki 'yan Najeriya kan daura alhakin faduwar Super Eagles da magana da Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Sai dai kuma abun bakin ciki shine yan wasan na Najeriya ba su taki sa'a ba inda aka yi masu ci daya mai ban haushi wanda hakan ya fitar da su daga gasar ta cin kofin na Afrika.

Ana haka, sai wasu yan Najeriya suka daura alhakin faduwarsu a kan wayar tarho da aka yi tsakanin tawagar yan wasan da shugaban kasar kafin fara wasan.

A martaninsa, Kurfi, wanda ya kasance mamba a kwamitin fasaha na NFF ya caccaki irin wadannan ‘yan Najeriya inda ya ce kawai suna kai hare-haren wuce gona da iri ne, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jihar Kebbi: Yadda 'yan bindaga suka hallaka da dama, tare da sace wasu saboda kin biyan haraji

Kurfi ya ce:

"Daura laifin faduwar Super Eagles a kan shugaban kasa bai da wani amfani kuma abun dariya ne a takaice. Wadanda ke irin wannan sharhi na wauta sun yi batan hanya ne. Ban ga wata alaka tsakanin hirar shugaban kasa da kayen da Super Eagles suka sha ba.
"Zance na gaskiya, shugaban kasa ya ware lokaci don tattaunawa da tawagar duk da dumbin aikin da ke gabansa, don haka kamata ya yi a jinjina masa. Bai kamata yan Najeriya su dauki wannan goyon baya da Shugaban kasa ya yi a banza ba.”

Ya ce maimakon haka, kamata ya yi yan Najeriya su samu lokaci su yi wa Eagles addu'an samun nasara a wasanninsu na gaba.

Ya ce:

"Super Eagles ba su gaza ba. Kawai dai bacin rana suka samu. Idan nasara ba a wajenka take ba, babu yadda ka iya.
"Maimakon daura laifin kashin da suka sha kan wani, ina bukatar yan Najeriya da su yi wa tawagar addu'an samun nasara a gaba. Kada mu bata lokaci da ta da jijiyan wuya kan abun da ya riga ya faru."

Kara karanta wannan

AFCON: Kai tsaye Buhari ya kira zakarun Super Eagles, ya kara musu karfin guiwa

Buhari: Ka da 'Yan Najeriya su cire tsammani daga Super Eagles

A gefe guda, mun ji cewa bayan ci daya mai ban haushi da Tunisiya ta yi wa Najeriya a gasar cin kofin Afrika a Garoua, kasar Kamaru, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki yan Najeriya da kada su cire tsammani daga tawagar da jami’anta.

A cewar Buhari, koda dai tawagar basu kai ga tsammanin yan Najeriya ba a gasar, daga jami’ai har yan wasan sun cancanci a yaba masu kan gwagwarmayar da suka yi, rahoton NTA News.

Babban mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin labarai, Garba Shehu, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a daren Litinin, 24 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel