Da Duminsa: Kungiyar Barcelona ta raba gari da mai horad da yan wasa, Ronald Koeman

Da Duminsa: Kungiyar Barcelona ta raba gari da mai horad da yan wasa, Ronald Koeman

  • Kungiyar Barcelona ta sanar da sallamar kocinta, Ronald Koeman, daga mukaminsa na mai horarwa
  • Barca ta dauki wannan matakin ne ranar Laraba da daddare bayan ta sha kashi a hannun Rayo Vallecano
  • Ana tsammanin kungiyar zata maida hankali wajen maye gurbinsa da tsohon dan wasan ta, Xavi Hernandez

Spain - Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sallami mai horad da yan wasanta, Ronald Koeman, bayan ta sha ka shi a hannun Rayo Vallecano.

Barcelona ce ta sanar da haka a shafinta na yanar gizo, bayan rashin nasarar da ta yi, ya maida ita mataki na 9 a teburin gasar Laliga ta kasar Spain.

Channels tv tace Kungiyar ta samu nasara ne a wasanni biyu daga cikin 7 da ta fafata karkashin mai horar wa Ronald Koeman.

Read also

Take hakkin dan Adam: UN ta aiko wa Najeriya wasika, ta bukaci bayanai 5 game da kamen Kanu

Ronald Koeman
Da Duminsa: Kungiyar Barcelona ta raba gari da mai horad da yan wasa, Ronald Koeman Hoto: Fabrizio Romano
Source: Facebook

Daga cikin wasannin da ta sha kaye har da babban wasan hamayya na Elclasico, wanda ta fafata da Real Madrid ranar Lahadi a gida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta shiga matsala

Rashin fara gasar Laliga da kafar dama ya jawo ana tsammanin zai wahala kungiyar ta samu tikitin shiga gasar zakarun nahiyar turai a shekara mai zuwa.

Kuma hakan zai sake jefa kungiyar cikin gagarumar matsala duk da wacce take ciki ta matsalar kudaden shiga.

A jawabin Barcelona, tace:

"FC Barcelona ta raba gari da mai horar wa Ronald Koeman a matsayin kocin yan wasan ta na da daddaren nan."
"Shugaban kungiya, Joan Laporta, ya sanar masa da matakin bayan rashin nasara a hannum Rayo Vallecano, Zai yi jawabin bankwana ranar Alhamis."
"Barcelona tana godiya da aikin da ya mata kuma tana masa fatan Alheri da nasara a nan gaba."

Read also

Da duminsa: An bindige Damina, dan bindigan da ya kona mata da ran ta a Zamfara

Su wa ake tsammanin zasu gaje shi?

Tsohon dan wasan Barca na tsakiya, Xavi Hernandez, wanda yake horad da kungiyar Al Sadd ta Qatar a halin yanzun da kuma kocin River Plate, Marcel Gallardo, sune ake tsammanin kungiyar zata fi maida hankali a kan su.

A wani labarin kuma mun tattaro muku kasashe 10 da Cristiano Ronaldo ya jefa wa kwallaye uku rigis a raga

Fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa ɗan asalin kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya kafa sabon tarihi a fagen zura kwallo uku a wasa ɗaya.

Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya zura kwallo uku rigis a wasa ɗaya yayin da yake wakiltar ƙasa.

Source: Legit.ng

Online view pixel