Sabon tarihi: Jerin kasashe 10 da Cristiano Ronaldo ya jefa wa kwallaye uku rigis a raga

Sabon tarihi: Jerin kasashe 10 da Cristiano Ronaldo ya jefa wa kwallaye uku rigis a raga

  • Fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa ɗan asalin kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya kafa sabon tarihi a fagen zura kwallo uku a wasa ɗaya
  • Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya zura kwallo uku rigis a wasa ɗaya yayin da yake wakiltar ƙasa
  • A halin yanzun, ɗan wasan yana taka leda ne a ƙungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ƙasar Ingila

Portugal - Shahararren ɗan wasan kwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo, ya kafa sabon tarihi a fagen wasan tamaula ranar Talata data gabata.

Ɗan wasan ya zama ɗan wasa na farko da ya ci kwallaye uku rigis sau 10 a wasannin da ya taka wa ƙasarsa ta Portugal.

Aminiya ta rahoto cewa fitaccen ɗan wasan ya kafa wannan tarihin ne a wasan da ƙasarsa ta gwabaza da Luxembourg.

Kara karanta wannan

Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo ya zama shugaban ƙasa a 2023 ba, Dokpesi

Cristiano Ronaldo
Sabon tarihi: Jerin kasashe 10 da Cristiano Ronaldo ya jefa wa kwallaye uku rigis a raga Hoto: planetfootball.com
Asali: UGC

Ronaldo ya zura kwallo biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga yayin da ya karisa ta uku da kai, a wasan neman gurbin shiga gasar kofin Duniya.

Sabon tarihi a fagen zura kwallaye uku

Nasarar da Ronaldo ya samu na zura kwallo uku a ragar Luxembourg, ya kasance karo na 58 da ya yi irin wannan bajintar a wasa ɗaya a tarihin rayuwar kwallonsa.

Hakazalika da wannan nasara ne ɗan wasan ya zama na farko a tarihin kwallon kafa da ya zura kwallo uku rigis sau 10 a gida, wato kasarsa.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin ƙasashe 10 da Cristiano ya zuba wa kwallaye uku a wasa ɗaya.

1. Northern Ireland

Ronaldo ya yi bajintar zura kwallo uku a ragar Northern Ireland, yayin da suke karawar neman gurbin shiga kofin duniya na shekarar 2014.

Kara karanta wannan

Wani matashi ya hallaka ɗan shekara 50 da ya kama a dakin budurwarsa suna biɗala

2. Sweden

Ɗan wasan ya maimaita irin wannan bajinta a wasan fidda gwani na kofin Duniya tsakanin Portugal da Sweeden a shekarar 2014.

3. Armenia

Fitaccen ɗan wasan, wanda ke taka leda a Manchester United, ya ci kwallo uku rigis a wasansu da Armenia na share fagen shiga gasar Euro 2016.

4. Andora

A shekarar 2016, Ronaldo ya zura kwallo uku a ragar Andora, yayin da suke fafatawar neman shiga gasar kofin Duniya na 2018.

5.Tsibirin Faroe

Hakanan a 2017 yayin wasan neman shiga kofin Duniya na 2018, Ronaldo ya zura wa tawagar kwallon kafa ta Tsibirin Faroe kwallaye uku a raga.

6. Spain

Bayan fara gasar cin kofin Duniya na 2018, Ronaldo ya jefa kwallaye uku a ragar da golan Manchester United, David Degea na ƙasar Spain yake tarewa.

7. Switzerland

A gasar Uefa Nations League wanda Portugal ta lashe a shekarar 2019, Ronaldo ya zura wa ƙasar Switzerland kwallo uku.

Kara karanta wannan

Rahoto: Sojoji 10 da wasu mutum 21 sun mutu a harin yan bindiga cikin mako ɗaya a Najeriya

8. Lituania

A wasan shiga gasar kofin nahiyar Turai 2020, ɗan wasan ya sake irin wannan bajinta a wasansu da Lituania.

9. Lituania

Ya sake zura wa ƙasar Lituania kwallaye uku rigis a shekarar 2019, a wasan share fagen shiga gasar kofin turai.

10. Luxembourg

A ranar Talata da ta gabata, Ronaldo ya ci kwallon uku rigis karo na 10, a wasan Portugal da Luxembourg na shiga kofin duniya da za'a fafata a Gatar 2022.

A wani labarin na daban Kotu ta bada umarni a daure ‘Dan wasan Bayern a kurkuku saboda tsohon rikici da Budurwarsa

Marca tace tauraron Bayern Munich, Lucas Hernandez zai iya shafe watanni shida a gidan maza saboda saba umarnin da kotu ta yi masa a 2017.

A farkon shekarar 2017 ne jami’an tsaro suka kama ‘dan wasan a sakamakon kwantar da wata budurwarsa da aka yi a asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel