Siyasar Najeriya
Sakataren jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kwara, Alhaji Rasaq Lawal, ya yi murabus dagan kan muƙaminsa. Alhaji Lawal ya kuma fice daga PDP.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da gwamnonin jihohin Imo, Ogun da Kwara a fadarsa Aso Villa da ke Abuja.
Fasto Godwin Ikuru ya shawarci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyar LP, Peter Obi da kada ya bari sai ya yi rashin nasara a kotu kafin ya taya Tinubu murna.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai tura sunayen sabbin ministocin da zai naɗa gaajalisar tarayya tsakanin ranar Laraba da Alhamis idan ba a aamu canji ba.
Gidan tsohon shugaban APC da ya saba ganin ‘yan siyasa, ya koma dandalin jami’an tsaro kuma EFCC za tayi binciken kan zargin da ake yi na facaka da N30bn a NWC.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na jihar Gombe ya rantsar da Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi a matsayin babban sakataren gwamnatin jihar (SSG) a karo na biyu.
A wadanda za su iya karbar kujerar Abdullahi Adamu a APC akwai Sanata Tanko Umaru Almakura, wani na-hannun daman Bola Tinubu da kuma wani tsohon Gwamnan Filato.
Tsohon 'dan majalisa, Sanata Shehu Sani ya yi martani ga murabus din Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun ayyana sunan wanda ya dace da kujerar shugaban APC mai ci. A cewarsu babu wanda ya dace irin Abdullahi Umar Ganduje.
Siyasar Najeriya
Samu kari