Karshen Mulkin Buhari: Manyan Alkawura 3 da Shugaba Buhari Ya Yi Amma Ya Gaza Cika Su

Karshen Mulkin Buhari: Manyan Alkawura 3 da Shugaba Buhari Ya Yi Amma Ya Gaza Cika Su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kan gargarar sauka daga mulki a karo na biyu a ranar 29 ga watan Mayu, inda zai mika mulki ga sabon shugaban kasa.

Tuni masana siyasa suka fara duba da waiwaye ga abubuwan da Buhari ya yi alkawarin yi da kuma dasa alamar tambayar shin ya yi su tun farkon hawansa a 2015 zuwa yanzu?

Ana yaba Buhari wajen samar da ababen more rayuwa, gine-gine da farfado da lalatattun tituna da layukan dogo, amma yaya ayek gani a fannin tattalin arziki da tsaro?

Shugaba Buhari ya gaza cika alkawura 3 da ya dauka
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mu fara da fannin tsaro

Kafin zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015, babban abin da ya tsaya a wuyan ‘yan Najeriya kamar kashin kifi shine matsalar tsaro, musamman rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Zaben Majalisa: An Bar APC Da Ciwon Kai, Mutanen Arewa Maso Yamma Sun Huro Wuta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fallatsar kananan makamai da kuma tashe-tashen hankulan da suka shafi kalibanci na da nasaba da yawaitar fadadar ta’addanci a yankin Arewa ta Tsakiya a wancan lokacin.

Bata sauya zane ba, a cikin shekaru 8 na mulkin Buhari, Najeriya na fama da fada tsakanin makiyaya da manoma, da kiyayya tsakanin kabilu a Arewa ta Tsakiya.

Garkuwa da mutane don karbar fansa ya zama wata kasuwa mai samar da riba mai kwabi a mulkin Buhari, sata a tekun kasar da kuma 'yan‘bindiga a Kudancin Najeriya duk sun zama ruwan dare a mulkin Manjo.

Mu dawo fannin rashawa

Najeriya bata shaida wani sauyi ba wajen yaki da cin hanci da rashawa a mulkin Muhammadu Buhari na shekaru 8.

A cewar kididdigar rashawa ta Corruption Perception Index a 2022, Najeriya ce kasa ta 150 cikin kasashe 180 da suka fi rashawa a 2021.

Kara karanta wannan

An Bar ‘Yan Najeriya Cirko-Cirko, Sudan ta Hana Mutanen Afrika Ficewa a Tsakiyar Yaki

A takaice, daga hawan Buhari a 2015 zuwa yanzu, Najeriya bata sauka kasa daga ma’aunin rashawa ba, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Uwa-uba; tattalin arziki

Tattalin arzikin Najeriya ya jejjeme a karkashin mulkin shugaba Buhari na shekaru 8 kacal, ‘yan kasar sun shaida haka.

Kasar ta fuskanci karyewar tattalin arziki har sau biyu, darajar kudin Naira ya sauka kasa da 800% sannan zaman kashe wando ya karu da 33.3% a kasar.

Baya ga karin farashi a fannin kayayyakin makamashi da kuma yadda kamfanoni ke garkame kofofinsu na aiki, bashin da ake bin Najeriya yanzu ya kai Naira tiriliyan 44.

Ana kuma hasashen bashin zai shilla zuwa Naira tiriliyan 77 idan aka gwama da bashin Naira tiriliyan 23 da gwamnatin Buhari ta ci a hannun babban bankin kasar; CBN.

Sharhin masani game da kokarin da Buhari ya yi daga 2015 zuwa 2023

Yayin da yake sharhi game da kokarin Buhari da gwamnatinsa, masanin siyasa kuma mai sharhi a kanta, Okanlwawon Gaffar ya ce Buhari ya ci maki 50 cikin 100 na ayyukan kirki ga Najeriya.

Kara karanta wannan

Yakin Sudan: Peter Obi Ya Yi Tuni 1 Mai Muhimmanci Ga Shugaba Buhari

A cewarsa:

“Gwamnatin Buhari ta yi matukar kokari wajen ayyukan gine-gine da gyare-gyare. Akalla gwamnatin ta yi nasarar yin wasu manyan ayyuka.
“Sai dai, a fannin tattalin arziki da tattala masu zuba hannun jari daga kasashen waje, bai tabuka abin a zo a gani ba.”

A kwanakin baya Buhari ya nemi afuwar 'yan Najeriya daidai lokacin da mulkinsa ke zuwa karshe a watan gobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel