Zance Ya Kare, Jakadan Najeriya Ya Fadi Gaskiyar Alakar Tinubu da Kasar Guinea

Zance Ya Kare, Jakadan Najeriya Ya Fadi Gaskiyar Alakar Tinubu da Kasar Guinea

  • Bayanai sun kara fitowa game da Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban Najeriya kan yiwuwar kasancewarsa dan kasar Guinea
  • Ambasada Ousmane Yara, jakadan Najeriya a kungiyar gamayyar Afrika ya ce, shugaban Guninea a 2016 ya taba gayyatar Tinubu zuwa kasarsa
  • Yara ya bayyana cewa, ba Tinubu shaidar zama dan kasa Guinea ba komai bane face karramawar tasirinsa ga tattalin arzikin kasar

FCT, Abuja Jakadan Najeriya a kungiyar gamayyar Afrika, Ambasada Ousmane Yara ya bayyana alakar Bola Tinubu da kasar Guinea.

Bayanan Yara suna zuwa bayan da wani bidiyo ya yadu da ke nuna Tinubu da gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu a cikin wani jirgi mallakin gwamnatin Guinea, rahoton Daily Sun.

A cewar Yara, an dauki bidiyon ne a 2016 a lokacin da Tinubu ya ziyarci shugaban kasar Guinea a bikin ‘yancin kan kasar. Ya kuma bayyana cewa, ziyarar ta 2016 ce ta biyu a Tinubu ya kai kasar Guinea.

Kara karanta wannan

29 Ga Watan Mayu: Ministan Buhari Ya Bayyana Abu 1 Tal Da Zai Iya Hana Rantsar Da Tinubu

An fadi alakar Tinubu da kasar Guinea
Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Babu alakar Tinubu da kasar Guinea

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, Yara ya bayyana cewa, babu wata alakar kasancewa da alaka mai karfi tsakanin Tinubu da shugaban kasar, Alpha Conde.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar jakadan, gwamnatin Conde ya ba Tinubu shaidar zama dan kasa ne don martaba shi ba don ya kasance asalin dan kasar ba.

A kalamansa:

“Tinubu ya yi kwana daya ne kadai kuma ya ya wuce Landan daga can, amma ya bar tawagar da ya zo da ita don ci gaba da tattaunawa da jami’an Guinea game da yadda za a ciyar da Guinea gaba.
“Tawagar da jami’an gwamnatin Guinea sun yi aiki tare na tsawon kwanaki uku, kuma sun zo da matsaya ga tattalin arzikin kasar.”

Ya kara da cewa, ziyarar Tinubu ta farko zuwa kasar ta kasance 2015, inda kafin nan ya karbi bakuncin shugaban na Guinea a Legas, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Bayan shafe kwanaki a kasar waje, Tinubu ya dawo Najeriya

Yara ya bayyana cewa, a lokacin da hakan ya faru, Sanwo Olu bai zama gwamnan Legas ba, kuma sukan yi tafiye-tafiye zuwa kasashe, ciki har da halartar bikin ‘yancin kai na Guinea.

Babu wanda ya isa ya hana rantsar da Tinubu

A wani labarin kuma, jigon APC ya bayyana cewa, babu wanda ya isa ya hana rantsar da Bola Ahmad Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Wannan na zuwa ne bayan da wasu ke kokarin kawo tsaiko ga yadda za a rantsar da Tinubu ya karbi mulki daga hannun Buhari.

Ana ci gaba da cece-kuce game da rantsar da Bola Ahmad Tinubu a Najeriya, lamarin da ke ci gaba da jan hankalin jama’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel