Siyasar Najeriya
Dakarun rundunar yan sanda sun garzaya sun kwace iko da zauren majalisar dokokin jihar Abiya bayan rikicin shugabancin da ya balle har ake kokarin cire kakaki.
Mambobin majalisar dokokin jihar Abia sun yi zama a wani wuri da ba'a sani ba kuma 18 daga cikin 27 sun kaɗa kuri'ar tsige shugaban majalisa, Chinedum Orji.
Tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya ce ƙasar nan ta tafka babbar asara rashin samun mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a matsayin shugaban ƙasa.
Peter Obi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), ya musanta cewa ya sanya labule da Bola Tinubu. Obi ya ce labarin ƙanzon kurege ne kawai.
Tsohon kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta reshen jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari, ya musanta zargin karban na goro domin ayyana Aishatu Binani.
Tsohon ministan Niger Delta kuma zaɓabɓen sanata, Godswill Akpabio, ya gana da shugaba Buhari. Sanatan ya gaya masa aniyar sa ta son zama shugaban majalisa.
Gwamnan jihar Imo mai neman tazarce a inuwar APC, Hope Uzodinma, ya musanta rahoton da ke yawo cewa yan bindiga sun farmaki ayarinsa har sun kashe yan sanda.
Rundunar yan sandan ƙasa da ƙasa ta aike da sammaci ga dakataccen kwamishinan zaben jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, kan abinda ya aikata lokacin cikon zabe.
Ganduje ya yi martani mai zafi ga Kwankwaso game da kafa sabbin masarautun jihar Kano da a halin yanzu suke guda biyar sabanin daya da aka sani a shekarun baya.
Siyasar Najeriya
Samu kari