Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Babban Sakataren Gwamnati, Ya Kaddamar Da Kwamitin Mutum 10 Na Masu Ba Shi Shawara

Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Babban Sakataren Gwamnati, Ya Kaddamar Da Kwamitin Mutum 10 Na Masu Ba Shi Shawara

  • Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya sake daukar rantsuwa domin kama aiki a matsayin babban sakataren gwamnatin jihar Gombe
  • Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya rantsar da Njodi a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli, kuma wannan ne karo na biyu da yake rike mukamin
  • Gwamnan ya kuma kaddamar da wani kwamitin mutum 10 na masu ba shi shawara kan yadda za a tafiyar da harkokin gwamnati

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya rantsar da Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi a matsayin sakataren gwamnatin jihar (SSG) a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a kwanan nan ne gwamnan ya sake nada Ndoji a matsayin SSG bayan ya rike mukamin a gwamnatinsa na farko tsakanin 2019 da 2023.

Kara karanta wannan

An shiga matsi: Jerin gwamnoni 3 da suka ji tausayin talaka, sun kara albashin ma'aikata

Gwamna Inuwa Yahaya ya rantsar da sakataren gwamnatin jihar Gombe
Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Babban Sakataren Gwamnati, Ya Kaddamar Da Kwamitin Mutum 10 Na Masu Ba Shi Shawara Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

Ya bayyana Farfesa Ndoji a matsayin kwararren jagora wanda ya bayar da gagarumin gudunmawa a nasarorin da ya samu a mulkinsa na farko.

Da yake taya shi murna, gwamnan ya bukace shi da ya kara himma wajen karfafawa tare da aiwatar da yunkurin gwamnatinsa na samar da ingantaccen aiki ga al’ummar jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A martaninsa bayan daukar rantsuwar aiki, Farfesa Njodi ya bayyana cewa ya sake gogewa a aikin da ya yi tare da Gwamna Yahaya a cikin shekaru hudu da suka gabata, rahoton Nigerian Tribune.

Gwamna Inuwa Yahaya ya kafa kwamitin masu ba shi shawara

A halin da ake ciki, Gwamna Yahaya ya kaddamar da kwamitin mutum 10 na masu ba shi shawara domin jagorantar aiwatar da kyawawan manufofi da shirye-shiryen gwamnatinsa.

Mambabin kwamitin sun hada da; Farfesa Idris Mohammed wanda zai yi aiki a matsayin ciyaman; Dr Ibrahim Jalo Daudu; Malam Muhammad-Kabir Ahmad; Farfesa Baba Yusuf Abubakar.

Kara karanta wannan

Tarihi: Jerin gwamnoni 6 da suka taba yin mataimakin gwamna a jihohinsu

Sauran sune Dr Mika Ismaila Jimeta; Farfesa Fatima B.J. Sawa; Injiniya Saidu Aliyu Mohammed; Arc. Suleiman Mohammed Kumo; Injiniya Abubakar Bappah da Dr Mu’azu Shehu, shugaban sashin bincike da tattara bayanai wanda zai yi aiki a matsayin sakatare.

Da yake martani, Farfesa Mohammed ya yi godiya ga gwamnan a kan karfin gwiwar da yake da shi a kansu, yana mai basu tabbacin sauke nauyin da aka daura masu.

Buhari ya dawo gida Najeriya bayan halartan taron AU a kasar Kenya

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo gida Najeriya daga Kenya ana tsaka da tashin hankali a cikin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

An sanar da dawowar shugaban kasar Najeriya ne a cikin wata wallafa da kungiyar Tinubu/Shettima Media Support (TMS) ta yi a Twitter a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel