Abubakar Kyari: Muhimman Abubuwa 5 Game Da Sabon Shugaban Rikon APC Na Kasa

Abubakar Kyari: Muhimman Abubuwa 5 Game Da Sabon Shugaban Rikon APC Na Kasa

  • Tsohon sanatan jihar Borno, Abubakar Kyari ya zama sabon shugaban riko na jam'iyyar APC mai mulki na kasa
  • Hakan ya biyo bayan murabus din da tsohon shugaban jam'iyyar, Abdullahi Adamu ya yi a ranar Litinin
  • Kyari dai tsohon sanatan jihar Borno ne kuma da ga tsohon gwamnan Arewa ta Tsakiya, Birgediya Abba Kyari

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Abubakar Kyari, wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa na shiyyar Arewa, shi ne ya zama sabon shugaban riko na jam’iyyar na ƙasa.

Hakan ya biyo bayan murabus da tsohon shugaban APC Sanata Abdullahi Adamu ya yi daga matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Abubakar Kyari ya maye gurbin Abdullahi Adamu
Sanata Abubakar Kyari ne sabon shugaban riko na jam'iyyar APC na kasa. Hoto: Willy Ibimina Jim-george
Asali: Facebook

Kundin tsarin mulkin APC ne ya tsara hawan Kyari

Kamar yadda kundin dokokin jam’iyyar ta APC ya tsara, a yayin da shugaban jam’iyyar na ƙasa ya yi murabus, mataimakin shugaban jam’iyyar da ya fito daga shiyya ɗaya ne zai karɓi ragamar shugabancin.

Kara karanta wannan

"Har Yanzu Peter Obi Yana Da Sauran Dama": Faston Da Ya Hango Nasarar Tinubu Ya Kara Magana Mai Daukar Hankali

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An bayyana cewa Abubakar Kyari ya halarci wani taro da ya gudana a babbar sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja.

An kuma bayyana cewa taron ya kunshi masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta APC wanda shi Sanata Abubakar Kyarin ya jagoranta kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

A tare da Kyari a wajen taron da ya gudana a Abuja akwai, mataimakan shugaban jam'iyyar APC na kasa na duka shiyyoyi shida da ake da su a Najeriya.

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani kan Abubakar Kyari

1. Abubakar Kyari, wanda da ne a wurin marigayi Birgediya Abba Kyari, tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Arewa ta Tsakiya, an haife shi a ranar 15 ga Janairun shekarar 1960 a Jihar Borno.

2. Ya yi karatun digirinsa na farko a jami'ar Tennessee Martin da ke kasar Amurka. Bayan nan, a shekarar 1989, Abubakar ya halarci jami'ar Webster St. Louis Missouri, duk a kasar ta Amurka, inda ya yi digiri na biyu bangaren kula da kasuwanci.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Bayyana Yadda Na Hannun Daman Buhari Suka Tsinci Kansu A APC Bayan Zuwan Tinubu

3. An zabi Abubakar Kyari a matsayin dan Majalisar Wakilai a karkashin jam’iyyar UNCP a shekarar 1998. Haka nan kuma, an sake zabarsa a matsayin dan Majalisar Wakilai a karkashin jam’iyyar APP daga 1999 zuwa 2003.

4. Ya rike mukamin kwamishina a jihar Borno daga shekarar 2003 zuwa 2011. A shekarar 2015, an zabi Kyari matsayin Sanata mai wakiltar Borno ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC.

5. An sake zabarsa matsayin sanata a zaben shekarar 2019 inda ya rike kujerar har zuwa lokacin da aka nada shi mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa shekarar 2022.

Dalilin da ya sa Abdullahi Adamu ya yi murabus daga shugabancin APC

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan ainihin dalilin da ya sanya tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ya yi murabus.

An bayyana cewa ana zarginsa da badakalar wasu makudan kudade, wanda hakan ne ya sa wasu daga cikin jam'iyyar ta APC suka matsa masa lamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel